ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Adawa Da Tunanin Yakin Cacar Baki Da Siyasar Karamar Kungiya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Game da taron kolin Amurka da Japan da ake gudanar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kasashen Amurka da Japan ba su yi la’akari da damuwar Sin ba, sun yi wa Sin batanci a kan batun yankin Taiwan da abin da ya shafi ikon mallakar teku, kuma sun tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Sin.

Game da hakan, Sin ta nuna adawa, kuma ta yi kakkausar suka ga bangarorin da abin ya shafa. Sannan kuma bangaren Sin na adawa da tunanin yakin cacar baki da siyasar karamar kungiya.

  • Firaministan Kasar Sin Ya Jagoranci Taron Neman Ra’ayi Kan Aikin Tattalin Arziki
  • Xi Jinping Ya Gana Da Ma Ying-Jeou A Beijing

Game da sanarwar da shugaban Amurka Joe Biden ya fitar bayan da ya gana da firaministan Japan Fumio Kishida, Mao Ning ta bayyana cewa, damuwar da Amurka da Japan suke nuna wa manufar makaman nukiliya ta Sin, ba ta da tushe, kuma tana da mugun nufi. Sin tana bin manufar kin yin amfani da makaman nukiliya a matsayin zabi na farko, ta yi wa kasashe da yankunan da ba su da makaman nukiliya alkawarin cewa, ba za ta yi amfani da makaman nukiliya a wuraren ba, ta dade da kiyaye karfin nukiliya a karamin matsayin da kasar take bukata, ba za ta shiga kowace takarar makamai ba. Idan dai wata kasa ba ta yi amfani da makaman nukiliya ga Sin ba, to ba za ta ga barazanar makaman nukiliya daga Sin ba.

ADVERTISEMENT

Game da Falasdinu a hukumance ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya sake duba bukatarta ta shekarar 2011 ta zama mamba ta MDD, Mao Ning ta ce, Sin na goyon baya ga Falasdinu wajen zama mamba ta MDD, kuma tana goyon bayan kwamitin sulhu ya gudanar da aikin da wuri.

Ban da wannan, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta fitar da wata takarda a yau, inda ta sanar da daukar matakin da ya dace kan wasu kamfanoni biyu na Amurka dake shiga ayyukan sayar da makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin.(Safiyah Ma)

LABARAI MASU NASABA

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

Sin
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

    An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”

MASU ALAKA

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin
Daga Birnin Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

July 25, 2026

Next Post
PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor Osimhen 

PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor Osimhen 

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

July 26, 2026
Sin

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi

July 26, 2026
Bala Mohammed

Sadakin Budurwa ₦3,000 Na Bazawara ₦1,500: Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaryata Batun

July 26, 2026
Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

Arewa Ta Rasa Alƙiblarta – Dattawan Arewa

July 26, 2026
Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

July 26, 2026
Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000  A Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna

July 26, 2026
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026
Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

July 25, 2026
Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

July 25, 2026
Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.