Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa APC da PDP dan juma ne da dan jummai sun gaza, a yanzu jam’iyyarsa ce kadai mafita ga ‘yan Nijeriya.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya bayyana hakan ne a wurin babban taron jam’iyyar NNPP na kasa da ya gudana a Abuja.
- Liu Yuxi Ya Halarci Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kan Sin Da Afirka Karo Na Uku
- Ya Kamata Jama’a Su Hada Kai Don Ciyar Da Nijeriya Gaba – Tinubu
Babban taron jam’iyyar ya samu halartar mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar da shugabanninta na jihohi 36 ciki har da na Abuja da ‘yan majalisun jihohi, wanda aka tabbatar da zaben Ajuji Ahmed a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa tare da tabbatar da kundin tsarin jam’iyyar da kuma sauya alaman tambarin jam’iyyar.
Kwankwaso ya siffanta APC da PDP a matsayin taron tsintsiya babu shara, wanda suka tara jiga-jigan ‘yan siyasa marasa amfani tare da kawo kuncin rayuwa ga ‘yan Nijeriya. Ya ce PDP jam’iyya ce da ta gaza, yayin da a yanzu gazawar APC ya fito kuru-kuru.
Ya tabbatar da cewa NNPP ce jam’iyya daya tilo da take kara bukasa a Nijeriya wacce ta fahimci muhimmancin ilimi wajen kawar da fatara da kuncin rayuwa da kuma yadda za a tsare rayukan da dukiyoyin ‘yan Nijeriya, ta hanyar tabbatar da hadin kai da kawo zaman lafiya da kuma wadata ga daukacin ‘yan Nijeriya.
“Dukkanmu mun san cewa PDP ta gaza. Mafi yawancinmu mun yanke shawara a tsakanin 2014 da 2015 mu kawo sauyi mai ma’ana. Abun takaicin dai shi ne, mun ga abubuwan da suka faru a tsakanin 2015 har zuwa yau. Wannan babban abun kunya ne ga gwamnatin APC. Saboda haka, mu a wurinmu, mun tabbatar da cewa APC ta gaza. Mun yi imani da cewa wannan kasar tana bukatar samun sauyi daga APC da PDP, kuma jam’iyyar NNPP ce kadai mafita, domin ita ce a yanzu take bunkasa a duk fadin kasar nan.
“Haka kuma na tabbatar da cewa wannan shi ne kyakkyawan fata kamar yadda muka tsaya a yau. Mafi yawancin bangarorin kasar nan, musamman yankin Arewacin Nijeriya, yanki da na fito, mafi yawan mutane an kore su daga gidajensu, sannan an kashe mutane da dama. A yanzu haka wasu suna raywa ne a cikin dazuka sakamakon garkuwa da su da ‘yan bindiga suka yi da kuma sauran ayyukan ta’addanci. Sannan mafi yawancin mutane ba sa damuwa da hakan. Abun sauki ne a yi garkuwa da mutane a gidagensu ko kan hanya ko kuma a kasuwa. Na tabbatar da cewa a kasar nan ne kadai ake irin wannan mummunan dabi’a. Hakkin gwamnati ne ta kare rayuwakan ‘yan kasa da kuma dukiyoyinsu.
“A matsayina na tsohon ministan tsaro kuma babban hafsan tsaro na Jihar Kano tsawon shekara 8 na tabbatar kuna da kayan aiki da jami’an tsaro da za su iya kawo tsaro a kasar nan. Wannan dama ce a gare ni wajen ganin mun hada kai mun yi karfi na ceto Nijeriya. Ina mai tabbatar da cewa za a ci gaba da samun hadin kai a cikin wannan jam’iyyar tamu. Za a ci gaba da yi wa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar adalci. Za mu ci gaba da gudanar da zaben fitar da gwani a wannan jam’iyya domin bai wa kowa damar samun matsayi.
“Ina godiya ga dukkaninku da kuka zabe ni a matsayin jagoran jam’iyyar na kasa a jam’iyyarmu. Ina alfahari da hakan. Sannan ina mai tabbatar muku cewa zai yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da cewa wannan jam’iyya ta kara karfi sosai,” in ji Kwankwaso.