A yau Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin da ake ciki tsakanin Iran da Isra’ila, ta kuma yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankula, su kai zuciya nesa domin kaucewa sake ta’azzara yanayin zaman dar dar da ake ciki.
Ma’aikatar ta ce kara tabarbarewar lamura, alama ce ta mummunan tasirin rikicin Gaza na baya bayan nan, don haka abu mafi muhimmaci a yanzu shi ne maida kai wajen aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD mai lamba 2728, da gaggauta kawo karshen rikicin Gaza.
A daya bangaren kuma, Sin ta yi kira ga sassan kasa da kasa, musamman kasashen da ka iya yin tasiri a lamarin, da su taka kyakkyawar rawa wajen kare zaman lafiya da daidaito a yankin.