Babban layin tashar samar da wutar lantarki na kasa ya sake faduwa a karo na shida a shekarar 2024 da muke ciki.
Kamfanin samar da wutar lantarki guda daya ne kawai ke aiki a yanzu haka, lamarin da ya jefa daukacin Nijeriya cikin duhu.
- Majalisar Dokokin Kebbi Ta Dakatar Da Dan Majalisa Mai Wakiltar Birnin Kebbi Ta Arewa
- G-7 Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Iran Ta Kai Wa Isra’ila
Rahotanni sun ruwaito cewa layin ya sake faduwa cikin dare ranar Litinin.
Rahotanni sun ce a halin yanzu tashar tana samar da wutar lantarki mai karfin mega watt 266.50 ne gaba daya a fadin kasar nan.
Da yake tabbatar da faduwar layin wutar a cikin wata sanarwa, Jos Disco ya ce Katsewar da ake fuskanta a halin yanzu, ta samo asali ne daga cibiyar sadarwa ta kasa.
Kuma faduwar layin wutar ya afku ne da misalin karfe 02:42 na yau Litinin, wanda hakan ya sa aka samu katsewar wutar lantarki ga dukkan fadin Nijeriya.
Shugaban Kamfanonin, Friday Adakole Elijah, ya bayyana fatan cewa za a dawo da grid din don samar da wutar lantarki ga masu amfani da ita.