Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), ta yi nasarar kashe manyan ‘yan ta’adda Ali Dawud, Bakurah Fallujah, Mallam Ari, da wasu mayaka 30 a Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Edward Gabkwet ya fitar, ya ce rundunar ta kai hari ne kan maboyar ‘yan ta’addar ISWAP da ke kauyen Kolleram a gabar tafkin Chadi.
- Ka Sallami Duk Wanda Ya Gaza Kokari A Gwamnatinka – El-Rufai Ga Tinubu
- Kasar Sin Ta Kammala Wani Zagaye Na Gwajin Injin Din Rokar Mai Da Za A Iya Sake Amfani Da Shi
A cewarsa, rundunar ta gudanar bincike a yankin inda ta gano ‘yan ta’adda tare da kashe sama da 30.
“Daga cikin wadanda aka kashe akwai wasu manyan kwamandojin Boko Haram irin su Ali Dawud, Bakura Fallujah, da Mallam Ari,” in ji shi.
Ya ce harin na sama ya kuma lalata wa ‘yan ta’addan motoci, babura, da kuma makamai.
“Bayan samun bayanan sirri, an kai harin ta sama tare da yi musu ruwan bama-bamai, inda aka kashe sama da 30 daga cikinsu.
“An kawar da manyan jiga-jigan mayakan ISWAP kuma hakan zai rage tasirinsu,” in ji shi.
Ya ce nasarar da sojojin suka samu ta nuna aiki tukuru da suke yi na son kawar da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro da zaman lafiyar ‘yan Nijeriya.