Gwamnan Jihar Filato, Batista Caleb Mutfwang, ya ware kujerun zuwa aikin hajji kimanin 500 ga Musulmai masu karamin karfi a jihar don su sami sukunin sauke farali a wannan shekara.
Babban sakatare a hukumar jin dadin alhazai na Jihar Filato,Honarabul Dauda Garga, ne ya bayyana haka a tattaunawar da ya yi da wakilimmu a Jos fadar gwamnatin jihar a makon da ya gabata.
- An Lalata Haramtattun Rijyoyin Mai 7 Da Jiragen Ruwa 4 A Ribas
- NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2
Honarabul Garga, wanda yake magana ta bakin daraktatan aikin hajji na hukumar, Dakta S. Murtal Magaji, ya yaba wa gwamnan bisa karamcin da ya yi wa Musulman jihar.
Ya ce gwamnan ya biya karin kudin guzuri da hukumar jin dadin alhazai ta yi wa jihohi a kwanakin da suka gabata na naira miliyan daya da dubu dari tara da goma shatakwas (1.918) a kan kowanne maniyyaci da ya biya kudin aikin hajjin wannan shekara daga jihar.
Haka Kuma ya ce hukumar jin dadin alhazan jihar ta kammala duk wani shirye-shiryenta, abin da ya rage mata kawai shi ne na tantance maniyyata da yin masu aluran kiwon lafiya da kuma bita.
Babban sakataren ya ce hukumar ta sami nasarar sama wa mahajjatanta gida a Makka kusa da Harami don saukaka masu yin tafiya mai tsawo zuwa wajen gudanar da ibada.
Ya bukaci al’ummar jihar da su manta da bambancen siyasa da kabilanci da addini da ke sakaninsu su hada kansu su mara wa gwamnan baya don ya sami nasarar aiwatar da kyawawan manufofinsa na gina sabuwar Jihar Filato.