Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a ranar Lahadi don nuna adawa da zaman sojojin Amurka a Jamhuriyar Nijar da ke karkashin mulkin soja.
Dama dai, ana sa ran wata tawaga daga birnin Washington da ke Amurka za ta iso jamhuriyar Nijar cikin kwanaki kadan don shirye-shirye janye jami’an sojin Amurka da ke kasar.
- Kusan 90% Na Masu Amsa Tambayoyin Duniya Sun Yaba Da Gudummawar Da Sin Ke Bayarwa Ga Bunkasuwar Duniya Irin Na Kiyaye Muhalli, A Cewar Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN
- Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara
A ranar Juma’a ne Amurka ta amince da janye sojojinta fiye da 1,000 daga kasar ta Afrika inda Washington ta gina wani sansanin fiye dala miliyan 100 domin harba jiragen yaki marasa matuka.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula 24 ne suka gudanar da zanga-zangar a garin Agadez da ke yankin hamadar arewacin kasar, inda sansanin sojin saman Amurka suke da masauki tun gwamnatin baya ta farar hula.
“Wannan Agadez ce, ba Washington ba, sojojin Amurka ku koma gida,” yadda masu zanga-zangar suka rubuta a jikin alluna da tutoci.