Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron tattalin arzikin duniya da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Afrilu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Bisa gayyatar da Firaministan Netherlands, Mark Rutte ya yi masa.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3 A Kasuwa A Zamfara
- Sojoji Sun Lalata Masana’antar Sarrafa Burodin ‘Yan Ta’adda A Borno
Yayin ziyarar, shugaba Tinubu zai tattauna da Firaministan, sannan zai shiga taruka daban-daban tare da Mai Martaba, Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima ta Masarautar.
“Yayin da yake kasar Netherlands, shugaba Tinubu zai halarci taron kasuwanci da zuba jari a tsakanin Nijeriya da Netherlands wanda zai hada shugabannin kungiyoyi a kasashen biyu don gano damarmaki na hadin gwiwa, musamman a fannin noma da kula da ruwa wajen samar da sabbin hanyoyin samar da mafita mai dorewa ga ayyukan noma.
“Za a kuma tattauna da jami’an kasar game da ayyukan sarrafa tashar jiragen ruwa wadanda a duniya an san su da kwarewa a kai.
“Bayan tafiyarsa Netherlands, shugaban zai ci gaba da halartar wani taro na musamman na tattalin arzikin duniya (WEF) wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 28-29 ga Afrilu a Riyadh, Saudiyya.
“A taron tattalin arzikin duniya, wanda ya mayar da hankali kan Haɗin gwiwar Duniya, Ci gaba da Makamashi don Ci gaba, Shugaba Tinubu da mukarrabansa za su yi amfani da damar taron na sama da shugabanni 1,000 daga ‘yan kasuwa, gwamnati, da jami’o’in ilimi don shiga tattaunawa don ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci.”
Shugaba Tinubu zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.
A baya dai Tinubu ya halarci irin wannan taro a Saudiyya, inda ya gana da masu ruwa da tsaki don neman su zuba hannun jari a Nijeriya.