Dambarwar sanar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje daga Jam’iyyar APC a mazabarsa da ke Dawakin Tofa a Jihar Kano da sake sanar soke dakatarwar da babbar kotun Jihar Kano ta yi a farkon makon nan bayan da farko ta ce ta tabbatar, na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce inda har ma wasu sun fara tunanin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da yiwuwar ya hakura da Ganduje ya kama Rabiu Musa Kwankwaso a Jihar Kano.
Dama dai magoya bayan Ganduje ba su ji dadi ba lokacin da Kwankwaso ya gana da Tinubu a Birnin Paris na kasar Faransa kafin a rantsar da shi da kuma ganawar da suka yi a watan Yuni a fadar shugaban kasa bayan ya shiga ofis.
- Hajji: Saudiyya Ta Gargadi Kamfanonin Bogi Kan Aikata Damfara, Ta Jadadda Muhimmancin Biza Ga Mahajjata
- Duk Da Matsin Rayuwa: Hukumomi 7 Sun Kebe Wa Kansu Naira Biliyan 80.9 Na Jin Dadi
A karshin ganawar na watan Yuni, dan takarar jam’iyyar NNPP a zaben 2023 ya bayyana wa ‘yan jarida ceewa sun tattauna harkokin siyasa da kuma na shugabanci shi da Shugaban Tinubu. Har zuwa yau mataimaka Tinubu da na Kwankwaso ba su bayyana cikakken bayani kan wannan tattaunawar ba. Da wannan ne wasu suke gabin akwai lauje cikin nadi.
Daga adadin masu jefa kuri’a da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta fitar a zaben 2023 mutum 93, 469,008, Jihar Legas ce ta fi kowacce yawa da mutum 7,060,195, sai kuma Jihar Kano da ke mara mata baya da mutum 5,921,370. Wannan ya sa jihohin biyu suke da matukar muhimmanci ga kowane dan Takara.
Nasarar da jam’iyyar NNPP ta yi a kotun koli ta kara yin tasiri a bangaren siyasa kan abokiyar hamayyarta ta APC wanda Ganduje yake shugabanta.
A ra’ayin wasu, kamar yadda kuma wadanda suka ce sun dakatar da Ganduje daga APC suka ba da hujja a kai kan zargin cin hanci da rashawa, Tinubu zai iya fakewa da hakan ya ajiye Ganduje a gefe ya rungumi Kwankwaso. Wasu ma na ganin cewa da gangan aka tayar da wannan bincike domin a kawar da Ganduje a janyo Kwankwaso.
Bisa burin shugaban kasa na ci gaba da samun nasara a zaben 2027, dole yana bukatar mutanen da za su iya sama masa kuri’u masu yawa kamar irinsu Kwankwaso wanda ake ganin yana da tasirin siyasa a Jihar Kano.
Duk da haka, akwai jigon jam’iyyar APC wanda ya yi watsi da cewa Tinubu zai hakura da Ganduje ya rungumi Kwankwaso.
Ya ce, “Tinubu dan siyasa ne mai mayar da alkairi ga duk wanda ya yi masa wahala. Ba zai taba yarda ya watsar da mutane kamar irinsu Ganduje ba. Ya san cewa har yanzu Kwankwaso bai karaya ba da burinsa na zama shugaban kasa ba. Yana da matukar hatsari ya bari jam’iyyar APC ta tarwatse a hannunsa, saboda yana kadayin janyo dan siyasa kamar Kwankwaso ya shigo APC.”
Da yake tarbar shugabannin APC na Jihar Kano a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja, Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da shafa masa kashin kaji a matsayinsa na shugaban APC domin rage wa Tinubu karfi a yankin arewa maso yamma a zaben 2027.
Ya yi ikirarin cewa wannan siyasa ce domin kawar da hankalin mutane daga gazawar gwamnatin NNPP da ke jagorantar Jihar Kano. Ya ce lallai shugaban kasa ya tabbatar masa da cewa shi ne ya sani a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
A wannan gaba, wasu na ganin Ganduje yana da goyon bayan shugaban kasa ba zai taba yuwuwa ba a watsar da shi a kama Kwankwaso, yayin da wasu suke ganin an kisa wannan bincike ne domin tunbuke Ganduje daga shugabancin jam’iyya tare da janyo Kwankwaso a jiki.