Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai farmaki da daddare, a unguwar Dutse Makaranta da ke Karamar Hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya, inda suka yi garkuwa da akalla mutum biyar.
Daga bayanan da aka samu, ‘yan bindigar sun zakke wa al’ummar ne ta wani yanki mai tudu da ke da daura da yankin Mpape, wata al’umma a cikin Babban Birnin Tarayya Abuja.
- Sharhi: Bukatar Sake Farfado Da Kiwon Tarwada A Nijeriya
- Ta Hanyar Tinkarar Wannan Muhimmin Batu Ne Kawai Za A Iya Inganta Dangantakar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
An nakalto cewa ‘yan bindigar sun isa wata bishiyar mangwaro da ke wani yanki da ake kira New Jerusalem a Duste Makaranta da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin ya ce, “Daga irin bayanan da muka samu, masu garkuwar sun zo wannan unguwar ne da misalin karfe 8 na dare, inda suka yi garkuwa da mace daya, maza uku da maza biyu. An gano daya daga cikin yaran mai shekaru uku a daji a yau da safe,” in ji majiyar.
Majiyar ta ci gaba da cewa, abin takaici, mahaifiyar yaran da aka sace ta ci gaba da fuskantar tashin hankali yayin da masu garkuwan suka yi mata fyade, don haka aka kwantar da ita a asibiti domin kula da lafiyarta a wani asibiti da ke kusa saboda raunukan da ta samu.
Harin dai ya jefa al’ummar Dutse cikin fargaba tare da nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro da ke addabar yankin.