Rundunar ‘yansandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’anta sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar mota a unguwar Mararaba da ke jihar Nasarawa.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Sun Fasa Rumbun Ajiye Kayan Abinci A Abuja
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Abuja Tare Da Sace Mutum 5
Ta ce an kama mutanen biyu ne a ranar 23 ga watan Afrilu da laifin satar motoci a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Adeh ta ce wadanda ake zargin suna cikin jerin sunayen da ‘yansandan ke nema ruwa a jallo tun watannin da suka gabata.
A cewarta, an kama wadanda ake zargin a wani otel da ke jihar Nasarawa a lokacin da suke karbar kudaden da suka cefanar da motar.
Ta ce an kwato motoci biyar da kayayyaki da dama daga hannun wadanda ake zargin.
Adeh ta ce kwamishinan ‘yan sanda mai kula da birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, ya umarci mazauna garin da su dauki duk matakan da suka dace don kare dukiyoyinsu.
Kwamishinan ya yi alkawarin tabbatar da samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a birnin tarayya Abuja.
Igweh ya bukaci mazauna yankin da su sanya ido tare da yin amfani da layukan gaggawa na ‘yansanda wajen bayar da rahoton dukkan wash abubuwan da ba su dace ba ta wadannan lambobi 08032003913, 08028940883, 08061581938 da 07057337653.