Bayan ‘yan watanni da nada shi a matsayin mukaddashin darakta-janar na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Njeriya, (NCAA), Kyaftin Chris Najomo, na fuskantar zargin kashe kudi ba bisa ka’ida ba, da keta dokokin gwamnati.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, babban jami’in kula da harkokin sufurin jiragen sama bayan nada shi a mukamin mukaddashin hukumar a ranar 13 ga Disamba, 2023, Najomo ya kashe makudan kudade, inda ya sayi wata mota kirar Toyota Landcruiser 2022 da ta haura N250m, wacce ko a cikin kasafin kudin bana ba a saka ta ta ba.
- NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 1.8 Ke Dauke Da Cutar Kanjamau – Hukumar NACA
Wani mai mutum da aka sakaya sunansa ya kuntsawa jaridar Daily Nigerian cewa babu inda Majalisar Dokoki ta amince masa a kunshin kasafin kudin NCAA na ya sayo wannan mota ta musamman.
Hakazalika binciken Daily Nigerian ya nuna cewa an sayo motar SUV ne ba tare da amincewar hukumar kula da saye da sayar da kayayyaki ta kasa da majalisar zartarwa ta tarayya ba.