Shugaban Serbia Aleksandar Vucic, ya sha ganawa tare kuma da tattaunawa da shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma a cewarsa, a ko wane karo na ganawarsu akwai wani abin da ba zai iya mantawa da shi ba.
A shekarar 2016, kamfanin samar da karfe mai inganci da aka yiwa lakabi da “Alfanun Serbia” da aka kafa shi a yau shekaru dari da suka gabata, ya yi fama da karayar arziki, kuma a wannan muhimmin lokaci, shugaba Xi Jinping, da kamfanonin Sin, sun ba da tallafi don fitar da kamfanin daga mawuyacin hali, inda ma’aikata fiye da dubu 5 suka samu zarafin komawa guraben aikinsu.
- CMG Ya Kaddamar Shirin Musayar Al’adun Abinci Na Sin Da Faransa
- Hungary Na Sa Ran Ziyarar Xi Za Ta Bude Sabon Babi A Dangantakarta Da Sin
Ya ce wannan ba karo na farko ba ne da Sin ta baiwa kasarsa taimako, domin kuwa, a lokacin barkewar cutar COVID-19 a shekarar 2020, Aleksandar Vucic, ya gaza samun taimako bayan kokarin rokon wasu sassa, har ya kusan yin kuka. Amma ba zato shugaba Xi Jinping ya buga masa waya nan da nan, kana ya samarwa kasar Serbia tallafin jiyya iri daban-daban.
Aleksandar Vucic ya nuna godiya matuka, yana mai cewa: “Al’ummar Serbia ba za ta manta da taimakon da Sin ta samar musu a kan lokaci ba, muna bayyana matukar godiya, za mu mayar wa abokan Sinawa martani bisa kokarinmu.”
Ingantacciyar hulda tsakaninsa da Xi Jinping, ta gamsar da Aleksandar Vucic sosai, kuma ya kara fahimtar cewa, Sin mai tarihin fiye da shekaru dubu 5, na sauke nauyin dake wuyanta. Saboda haka, Aleksandar Vucic ya ce, “ina da shirin rubuta wani littafi don tunawa da huldarmu.” (Amina Xu)