Shugaba Bola Tinubu da masu taimaka masa sun dawo Nijeriya bayan shafe mako guda a Turai.
Hadimin shugaban kasa na musamman, Bayo Onanuga ne, ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau.
- Sojojin Nijar Sun Kama Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Nijeriya, Kachallah Mai Daji
- Gwamnatin Kano Ta Rattaba Hannu Kan Dokar Yin Gwaji Kafin Aure
“Barka da dawowa gida mai girma shugaban kasa,” kamar yadda ya wallafa.
Idan ba a manta ba makonni biyu da suka wuce shugaba Tinubu ya tafi kasar Holland inda ya gana da firaministan kasar, Mark Rutte.
Daga nan kuma ya garzaya zuwa Saudiyya don halartar wani taron tattalin arzikin duniya (WEF).
Daga bisani kuma ya sake tafiya turai domin halartar wani taron.
Idan za a tuna a ranar 22 ga watan Afrilu, shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa masarautar Netherlands a wata ziyarar aiki.
Kakakin shugaban, Ajuri Ngelale, ya ce ya ziyarci kasar Netherlands ne bayan gayyatar da firaministan kasar, Mark Rutte ya yi masa.
Bayan ya bar Netherlands, Tinubu ya wuce Birni Riyadh na kasar Saudiyya don halartar taron WEF daga ranar 28 zuwa 29 ga watan Afrilu.
An sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya da zarar an kammala taron, amma bai dawo ba wanda hakan ya sanya ‘yan adawa fara cece-kuce game da inda shugaban ya shige.