• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rawar Da Iyaye Ke Takawa Wajen Taimaka Wa ‘Ya’ya Cimma Burinsu Na Karatu (1)

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
Iyaye

Ilimin yaro ya fara ne daga gida saboda Iyaye sune malamai na farko da ke bada gudunmawa wajen dora tubalin koyon ilimi inda ake farawa da koya tarbiya ta gari.

Ana samun daidatuwar lamarin ne bayan da gida da makaranta sun kammala sa tarbiyar koyon iliminsu ta ‘ya’ya.

  • Masu Masana’antu Na Kasar Sin Sun Raba Fasahohinsu A Majalisar Dinkin Duniya
  • Yadda Bankuna Da Cibiyoyin Kudi Ke Tafka Asara Sakamakon Fara Amfani Da Fasahar Zamani Ta AI

Iyaye suna zama masu taimakawa ne wajen fafutukar/gwagwarmayar da suke yi wajen neman ilimi wajen kasancewa kamar sun yi tafiyar tare ne ta basu shawarwarin da suka dace.

Bada kwarin gwiwa da iyaye suke yin a taka muhimmiyar gudunmawa wajen samun cimma nasarar ‘ya’ya a matsayinsu na dalibai ko masu neman ilimi. Lamarin ba ya tsaya a gida ba ne har ma da makaranta gaba daya.

Lamarin ilimin yara na nasaba ne da yadda iyaye suke mu’amala da su a gida. Ga hanyoyi kadan wadanda iyaye za su yi amfani da su wajen ba ‘ya’yansu gudunmawa wajen samun ilimi.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

  1. Ku zama abin yin kwatancensu

Yara ko ‘ya’ya cikin sauki ne abubuwan da iyayensu suke yi ke basu sha’awa don haka ana bukatar iyaye su kasance abin da ‘ya’yansu za su yi koyi da su domin malaman ‘ya’yansu na farko, suna tare da su a gida abu na farko wurinsu ne za su koya.

A nuna masu yadda lamarin yake da ban sha’awa musamman ma rayuwar makaranta na iya kasancewa dakyau idan sun maida hankalinsu ga abubuwan da ake koya masu.Basu kwarin gwiwa su mai da hankalinsu wajen abubuwan da ake koya masu a ciki da wajen makaranta,da kasancewa wajen basu  shawarar da za ta taimaka masu.

2.Ku rika yin karatu tare da su

Yin aikin makaranta tare yana ba yara kwarin gwiwa su kasanace suna jin dadin kasancewa da kai domin za ka taimaka masu.Yin karatu tare wata hanya ce maikyau wajen kasancewa tare da su akan abin da ake koya masu a makaranta.

Wannan ko yin hakan ba kawai yana bunkasa masu sanin kalmomi kamar yadda ya dace ba da furta su,akwai ma kara masu sha’awar su kara mai da hankali wajen koyon fiye da yadda suka fara.Ziyartar dakin karatu tare da musayar littattafai masu inganci,domin taimaka masu karuwa da wani ilimin bayan wanda ake koya masu a aji.

  1. Ku rika duba ayyukan da suke yi

Yana da matukar dacewa iyaye su rika duba ayyukan da ‘ya’yansu suka yi a makaranta ko na gida.Ana iya gane ko ya halinsu yake idan aka duba irin yadda suke yi kan abubuwan da ake koya masu.

Basu shawara lokacin daya kamata da yi masu gyara kan abubuwan da suka yi da basu dace ba,tun lokacin suna yara a makaranta,da karafafa masu gwiwa su kasance nagari.

A taimaka masu wajen ganin sun mai da hankalinsu da isasshen lokaci na yin aikin da suka yi gida da kuma aikin da za‘a iya basu su yi a gida daga makaranta.

  1. Kar a cika masu ayyuka da yawa

Ba abin da ya dace bane a basu aiki mai yawa bama kamar lamarin da ya shafi koyo a gida.

Da yake kusan suna yin rabin lokacin da suke da shi a makaranta,kamata ya yi a taimaka masu wajen yin aikin da aka basu a makaranta idan sun dawo gida su yi.Don haka a taimaka masu wajen yin aikin da aka basu su yi a gida ba tare da lamarin ya dame su ba.

Lura da lokaci tsakanin aikin da za su yi a gida da,lokacin da za su yi wasa da hutawa hakan yana da amfani domin samun rayuwa mai inganci.

  1. Samar da yanayi mai kyau

Iyaye su tabbatar da cewa yara an samar masu wurin karatu da take da yanayi maikyau a gida.

A lura kada a rika yin ko a kauce ma maganar duk wasu matsaloli da suka shafi iyali  a gaban su yara,a kuma guje ma duk wani abin da zai kawo gardama a gaban su yaran.

Iyaye wato Uwa da Uba su gane cewa ilmin ‘ya’yansu abu ne da yake da muhimmanci, don haka su basu dukkan taimakon da suke bukata don su cimma buri ko nasara.

  1. A gaya masu gaskiya idan ba su yi dai dai ba

Idan kun lura ‘ya’yanku basu mai da hankali abubuwan da ake koya masu a makaranta,tun da farko idan an lura da hakan sai ayi masu gyara da yi masu bayanin yadda za su bullowa lamarin karatun kamar yadda ya kamata.

Sai dai kuma bai dace ku rika fadar kalmomin da za su sa hankalinsu ya ta shi,su daina sha’awa ko mai da hankalinsu kan darussan da ake kya msu a makaranta.A rika sa hakurim hulda da su,da kuma nuna masu hanyar da tafi dacewa su bi domin samun nasarar ko kawo gyara a wurin da aka lura da akwai matsala,a gaya masu abu maikyau da maras kyau maimakon a rika ganin laifinsu kowane lokaci.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
CMG Ta Zanta Da Firaministan Kasar Hungary

CMG Ta Zanta Da Firaministan Kasar Hungary

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.