Jarumar Kannywood, Mansura Isah na ci gaba da kare kanta kan zargin da wasu ke yi mata na cewa tana amfani da kasancewarta jarumar Kannywood wajen neman suna.Tana kokarin bata wa wata makarantar firamare suna, ta bayyana cewa an yi kunbiya-kunbiya a lokacin da suka tafi asibiti domin binciken lafiyar wasu yara da ta kama suna aikata ba daidai ba a wata makarantar firamare da ke Jihar Kano.
A wani faifan bidiyo da ta fitar a kwanikin baya, Mansura Isah ta yi kira ga iyayen yara a kan su kara sa ido kan tarbiyar ‘ya’yansu, musamman ma wadanda suke fita zuwa makarantu da kasuwanni. Ta ce abin da ta gani a wata makarantar firamare ya yi matukar tayar mata da hankali.
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
- Ya Kamata Manchester United Ta Kori Erik ten Hag?
Mansura ta yi ikirarin ganin wasu yara kimanin su 6 suna aikata badala yayin wata ziyarar da ta kai zuwa wata makarantar firamare. Ta ce ta shiga damuwa kasancewar yaran suna da kananan shekaru.
Wadannan kalamai da ta furta ya sa hukumar Hizba tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin, jarumar ta tabbatar da cewar kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin ya boye mata wasu daga cikin sakamakon binciken da aka yi a makarantar da kuma na asibiti.
Ta ce a lokacin da suka tafi makarantar mai yawan dalibai fiye da 6,000, daga nan aka ce dalibar da abin ya faru da ita ta fitar da wadanda suka aikata abin da ake zarginsu da aikatawa wadanda ta ce ‘yan aji 6 ne a makarantar, bayan ta fitar da su, sai suka dunguma zuwa asibiti domin gwajin lafiyarsu.
Bayan sun tafi asibitin tare da sauran ‘yan kwamitin, sai aka shiga da su dakin gwaji, inda ita kuma aka hana ta shiga. Bayan an kammala gwajin lafiyarsu, an hana ta ganin takardar sakamakon gwajin lafiyar da aka yi masu duk da cewa ya kamata a yi hakan kamar yadda Mansura ta tabbatar.