A wata gagarumar turjiya kan zabge wa mutane ‘yan kudadensu a asusun ajiyarsu da Babban bankin kasa, CBN ya ayyana da nufin tsaron yanar gizo na kudaden al’umma da ke asusun ajiyarsu, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da sa ido kan harkokin hada-hadar kudaden al’umma (SERAP) da BudgIT da ‘136 concerned Nigerians’ sun maka CBN a Kotu.
Kungiyoyin dai sun maka CBN a kotu ne saboda wani umarnin bankin na baya-bayan nan wanda ya umarci dukkan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi da su cire harajin tsaron yanar gizo ‘cybersecurity levy’ da kashi 0.5 cikin 100 akan duk wata hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo.
- Ecowas Za Ta Kafa Dakarun Ko-ta-kwana Don Yaki Da Ta’addanci
- Kabilar Bayankole Da Innar Amarya Ke Jima’i Da Ango Domin Gwaji
Umurnin, wanda aka bayar a ranar 6 ga Mayu, 2024, masu shigar da kara sun yi wa karar ta su da lakabi “Umurni ba bisa doka ba”.
A cewar Kolawole Oluwadare, mataimakin daraktan SERAP, zabge wa mutane ‘yan kudadensu daga asusun ajiyarsu, ya zarce ikon babban bankin na CBN.