Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a gaban kuliya bisa kashe Naira biliyan 18.96 wajen buga takardun kudi miliyan 684.5.
Tun da farko dai an shirya gurfanar da shi a ranar 30 ga watan Afrilu, 2024, amma aka dage zaman bayan yarjejeniyar da kotu ta yi da bangarorin EFCC da na Emefiele.
- Gwamnatin Nijeriya Ta Kafa Makarantar Bayar Da Horo Kan Al’adun Ƙasa – NICO
- Sojar Ukraine Ta Zama Bazawara Kwana Biyu Da Aurenta
A tuhume-tuhume hudu da EFCC ta shigar gaban kotun, ta yi zargin cewa Emefiele ya bijire wa umarnin doka lokacin sauya takardun Naira a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
EFCC ta kuma zargi Emefiele da cire Naira biliyan 124.8 daga asusun tara kudaden shiga na tarayya ba bisa ka’ida ba.
LEADERSHIP ta tattaro cewa tsohon gwamnan na CBN zai gurfana a gaban mai shari’a Maryann Anenih ta babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Wannan shari’ar za ta kawo adadin tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan na CBN zuwa uku.
A ranar 17 ga watan Nuwamba, 2023, Emefiele ya gurfana a gaban mai shari’a Hamza Muazu a kan tuhume-tuhume shida da suka hada da damfara, almundahana, wanda ya ki amsa laifinsa.
An kuma zarge shi da cin zarafin ofishinsa ta hanyar kwangilar sayen motoci 43 da suka kai Naira biliyan 1.2 daga 2018 zuwa 2020.
A ranar 8 ga watan Afrilu, 2024, EFCC ta kuma sake gurfanar da Emefiele tare da wani Henry Omoile a gaban mai shari’a Rahman Oshodi na kotun laifuffuka da ke Ikeja a Jihar Legas, kan zargin almundahanar dala biliyan 4.5 da Naira biliyan 2.8.
Sai dai Emefiele ya musanta wadannan tuhume-tuhume.
Rotimi Oyedepo (SAN) ne, ya sake shigar da sabuwar tuhuma a ranar 2 ga watan Afrilu, 2024 a madadin EFCC tare da wasu lauyoyi takwas da ke aiki da babban lauyan tarayya.