Kasurgumin dan bindiga, Usman Modi Modi, wanda aka fi sani da ‘Kartakwa’, ya mutu a ranar Talata tare da wasu yaransa hudu a wani kazamin artabu da suka yi da wani tsagin ‘yan bindiga a Jihar Katsina.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ibrahim Kaula ya aike wa LEADERSHIP a ranar Laraba.
Kaula, ya ce wata majiya ta bayyana cewa rikicin ya barke ne da misalin karfe 2:00 na rana, wanda ya hada da tsagin Modi Modi da kuma tsagin Abdulkarim Faca Faca a yankin Marina.
“A lokacin arangamar an kashe Usman Modi Modi da wasu yaransa hudu; Mankare, Gunki Ummadau, Dogo Jabi Birinya Bayan Dutsin na karamar hukumar Kurfi da Harisu Babba Yauni daga karamar hukumar Safana.
“A cewar majiyar, Usman Modi Modi da yaransa, sun mamaye yankin karamar hukumar Safana da Kurfi.
“Majiyar ta kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan irin su Usaini Yauni na karamar hukumar Safana da Abdulrahman Jankare Gangare na karamar hukumar Tsaskiya Safana, sun samu munanan raunuka a arangamar,” in ji sanarwar.
Kaula ya kara da cewa, ana ci gaba da kokarin cafke wadanda suka jikkata a yayin arangamar.