A wani mataki na cimma azamarsa na tsaron makamashi, tsaftar muhalli da rage kashe kudaden sayen man fetur, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci dukkanin ma’aikatu, sashi sashi da rassan gwamnati da su sayi motoci masu amfani da Makamashin iskar Gas (CNG).
A cewar kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, cikin wata sanarwa a ranar Litinin, umarnin shugaban na cikin matakin tabbatar da tsaftar muhalli da karfafa amfani Motoci Masu amfani da Makamashin iskar Gas wajen rage yawan kashe kudaden sayen fetur.
Da ya ke magana a zaman majalisar zartaswar gwamnatin tarayya, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa babu koma shirinsa na rungumar Makamashi.
“Wannan kasar ba za ta gaba ba muddin muka tsaya muna ta rawa a wuri daya. Yadda muka kuduri aniyar rungumar motoci masu amfani da Makamashin iskar gas a fadin kasar nan, dole mu yi yadda ofisoshin gwamnati za su zama abun misali wajen cimma wannan nasarar. Za ta fara daga mu kanmu, hakan zai nuna cewa mun dauki lamarin da muhimmanci daga bisani ‘yan Nijeriya za su biyo baya.”
Shugaban ya kuma ba da umarnin kin amincewa da duk wasu takardu da mambobin FEC suka gabatar na neman siyan motocin gargajiya da suka dogara da man fetur, inda ya umurci ’yan majalisar da abin ya shafa da su koma su nemi hanyoyin siyan motocin da suka dace da CNG.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaban kasar ya jajirce wajen amfani da karfin iskar gas ta kasa yadda ya kamata, tare da rage radadin tsadar sufuri a kan talakawa tare da inganta rayuwar dukkan ‘yan Nijeriya.