Ƴansanda sun cafke Rachel Geoffrey mai shekaru 23 bisa zarginta da laifin ƙona hannun ƴaƴan uwargidanta biyu a jihar Adamawa.
Rachel, na zaune ne a gidajen gwamnatin tarayya da ke Girei, ta yi sanadiyyar jin munanan raunuka a kan Genesis Geoffrey mai shekaru 7 da Ijadai Geoffrey mai shekaru 3. Da ma dai mahaifiyar yaran mai suna Rahila ta rabu da mahaifinsu a baya.
Rahotanni sun ce Rachel ta fusata ne bayan da yaran suka cinye abincin mahaifinsu da ta dafa ta ajiye masa. Daga nan ne ta ɗaure hannayen nasu da kyalle kafin ta cinna musu wuta.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Ɗankombo Morris ya shawarci iyaye da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kana ya kuma ba wa jama’a tabbacin yin bincike sosai kan lamarin.