Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta tsaro da bayar da ƙarin tallafi ga dakarun da ke yaƙi da ’yan bindiga a Zamfara.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Tsaro ta Jihar Zamfara a fadar gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an tattauna muhimman batutuwa kan matsalar tsaro a jihar da kuma hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa.
A cewarsa, taron ya samu halartar dukkan shugabannin hukumomin tsaro na jihar da suka haɗa da sojoji, ’yansanda, DSS, da dai sauransu.
Yayin da yake jawabi ga shugabannin hukumomin tsaro, Gwamna Lawal ya yaba wa sojojin bisa nasarorin da aka samu kawo yanzu a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda.
“Taron na yau zai duba yanayin matsalar tsaro da jihar ke fama da shi, da kuma tantance irin ci gaban da muka samu, da kuma tantance wuraren da ke buƙatar ƙara ƙaimi wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin jama’armu.
“Kamar yadda na sha nanata wa majalisar tsaro a ko da yaushe, fifikon gwamnatina shi ne tsaron rayuka da dukiyoyi. Don haka a ko da yaushe a shirye muke mu bayar da dukkan goyon bayan da ya kamata ga hukumomin tsaro daban-daban na jihar domin taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
“Ina so in gode wa Gwamnatin Tarayya da sojoji saboda tura ƙarin dakaru zuwa Zamfara. Wannan mataki na nufin kawar da duk ‘yan bindiga, kuma mun fara ganin sakamako.
“Na kuma yaba da nasarar cafke gungun masu garkuwa da mutane a Gusau tare da kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a faɗin jihar da suka haɗa da Gusau, Maradun, Kauran Namoda, da sauran ƙananan hukumomin. Waɗannan nasarorin da aka samu shaida ce da ke nuna tasirin ayyukan soji da ake yi a jihar.”