Wata babbar kotu da ke zaune a jihar Ekiti ta yanke wa wani mutum mai kimanin shekara 49, mai suna Akinola Ademola, hukuncin kisa ta hanyar rataya, saboda laifin kashe yayansa.
An gurfanar da Akinola, a gaban mai shari’a Lekan Ogunmoye a cikin watan Disamba, 2020, da laifin yin fashi da makami da kuma kisan kai.
An gabatar da shi gaban alkali cewa bayan, ya yi wa Akinola Tunde fashin mashin kirar Bajaj, mai lamba ADK 011 BC, lokacin da yake kokarin kwace wannan mashin din ya yi amfani da bindiga. A wannan lokacin ne ya kashe Akinola Tunde.
Wani wanda ya bayar da shaida, mai suna Ogunnusi Anike, wanda ya tabbatar wa da kotun cewa, “muna tare da wanda aka kashe din, a kan hanyar zuwa gona yana kan babur kirar Bajaj ni kuma ina tafiya a kasa, kawai sai na ga wani mutum ya fito daga daji da bindiga a hannunsa, ya harbi marigayi, sai na kwalla ihu na ce, “Tunde, Tunde, maza ka gudu ga wani nan zai harbe ka da bindiga”, ni ma sai na fara gudu, lokacin da nake gudu na ji karar bindiga, sai na hangi wani mutum yana wuce wa, da nake bayanin abin da ya faru da ni, sai ya ce mu je gurin, muna zuwa gurin sai muka ga gawar wannan mai mashin kuma an sace mashin din.
Mai gabatar da kara ya ce, wannan laifi ne da ya saba wa sashi na 402 (2) da 319(1) na dokokin manyan laifuka na dokokin jihar Ekiti na shekara ta 2012.
Da yake yanke hukunci mai shari’a Ogunmoye ya ce, kotu ta samu tabbacin aikata laifuka guda biyu, laifi na farko shi ne fashi da makami, sai na biyu kuma kisan kai.
Saboda haka, bayan tabbatar da wadannan laifuka guda biyu, kotu ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin fashi da makami da kuma kisan kai.