Wata zanga-zanga ta ɓarke a Kano yau Lahadi da nufin nuna rashin goyon baya da tsige Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, inda masu zanga-zangar suke neman a maido da shi kan karagar mulki.
Zanga-zangar wacce aka fara da misalin karfe 4:00pm na yamma bayan kammala addu’a a gidan Sarki da ke Nasarawa, cikin lokaci ƙanƙani ta ƙara faɗaɗa inda masu zanga-zangar suka buƙaci gwamnati da ta bi umarnin kotu tare da maido da Sarki Aminu bakin aiki.
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
- An Shawarci Sarki Aminu Ado Ya Fice Daga Kano
Abin mamaki shi ne akwai tarin jami’an tsaro a wurin amma ko kaɗan ba su yi wani yunƙurin hanawa ko taka musu burki ba duk kuwa da cewa suna kallo suke cinnawa tayoyi wuta tare da fasa allunan talla, lamarin da ya baiwa masu zanga-zangar damar cin karensu ba babbaka.
Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, sun yi ta rera waƙoƙin Sarki Aminu Ado tare da ɗaga kwalaye masu ɗauke da saƙonni irin su Abba Kabir Yusuf, Bi umarnin Kotu da “Aminu Har Yanzu Sarkin Mu Ne”. Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar Usaini Rabiu Kunya, ya jaddada yadda zanga-zangar tasu ta kasance cikin lumana, ya kuma buƙaci gwamnati da ta bi umarnin shari’a.
Wani mai zanga-zangar, Abubakar Garba, ya roƙi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya tabbatar da adalci a rikicin masarautar.
Zanga-zangar dai ita ce ta baya-bayan nan a rikicin da ya fara kunno kai jihar Kano bayan da majalisar dokokin jihar ta soke dokar da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Sarki Mohammad Sanusi II tare da ƙirƙiro ƙarin sabbin masarautu guda hudu.
Akwai yiwuwar samun ƙarin zanga-zanga a jihar Kano daga dukkan ɓangarorin biyu matuƙar jami’an tsaro ba su ta shi tsaye kan lamarin ba, wani abu da zai ƙara tasiri wajen dagula lissafi shi ne goyon bayan wani sashi daga jami’an tsaro.