Yayin da ‘Yan Nijeriya suka yi bikin ranar yara na shekara-shekara a farkon wannan makon, babu wani abu na a zo a gani da za a yi farin ciki game da bikin, bisa la’akari da mummunan halin da kasar ke fuskanta wanda yake dakushe fatan rayuwar yaran kasar ta gaba.
Gaskiyar abin da ke da ban mamaki shi ne, irin barazanar da ke neman lalata makomar rayuwar daukacin yara manyan gobe – tun daga sace-sacen da ‘yan ta’adda ke musu da yawaitar rufe makarantu zuwa ga yawaitar ayyukan karfi da ake sa yara da kuma aurar da kananan da ba su kai munzalin aure ba.
Maimakon kare hakki da walwalar yara da kuma ‘yan kasa masu karamin karfi, Nijeriya ta kasance a cikin rikicin da ke kawo cikas ga makomar kasar ita kanta.
- Ranar Yara Ta Duniya: Inganta Rayuwar Yaran Nijeriya Shi Ne Abu Mafi Girma – Tinubu
- ‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu
Akwai kididdiga mai sanyaya gwiwa game da ukubobin da suka dabaibaye yaran Nijeriya. Yara miliyan 18.3 ba sa zuwa makaranta, fiye da yawan daukacin al’ummar wasu kasashe.
Idan aka kwatanta da yawan wasu kasashen yadda ya kamata, adadin yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya ya zarce yawan mutanen kasashen Norway, Singapore, da Cuba. Wannan abin kunya ne kuma bai kamata a bar shi ya ci gaba ba.
A ra’ayin wannan jaridar, wannan mummunar shaida aka yi mana na kasancewa kasa mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya kuma wani tabo ne ga al’ummarmu.
A yankunan da ake fama da rikici musamman a arewa maso gabas da arewa maso yamma, neman ilimi ya zama jarumtaka mai hatsarin gaske, inda aka sace ko kuma aka yi garkuwa da yara sama da 1,600 a makarantunsu tun daga shekarar 2014, a cewar kungiyar da ke fafutukar kare lafiyar yara (Sabe the Children.
A cikin watanni uku na farkon shekarar 2024, sama da yara 200 ne ‘yan bindiga suka sace tare da yin garkuwa da su daga ajujuwansu a jihohin Kaduna da Sakkwakoto kadai.
Kamar yadda Daraktan UNICEF na Nijeriya Dr. Tushar Rane ya koka, an rufe makarantu 439 a duk fadin kasar a cikin 2023 saboda ko dai gwamnatoci sun karbe su suna amfani da su ko kuma tsoron kai musu hari.
A yankunan da ke fama da kashe-kashen na Boko Haram da kungiyoyin masu aikata laifuka, ana tilasta wa iyaye “zabi” mai wuya na ko dai su jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin hadari don samun ilimi ko kuma su bar su kara-zube cikin rayuwar jahilci da kuma karancin damar zama wani abu a rayuwa.
Wannan matsalar, ba za a iya jure wa zama a cikinta ba, domin tamkar wani mummunan rashin adalci ne da ke take hakkin yaran Nijeriya.
Bugu da kari, duk da haka fa, hare-haren da ake yi a kan makomar rayuwar yaran ba su kare a nan ba. Nijeriya ce kasa ta uku a yawan matan aure a duniya, inda aka aurar da mata miliyan 23.6 kafin su kai ga cika shekara 18 sannan sama da miliyan 10 kafin su kai shekaru 15, a cewar Asusun UNICEF.
An hana su samun ilimi tun a lokacin yarintarsu, wadannan ‘yan matan da ke cikin ukubar rayuwa sun zama kamar wadanda aka yanke musu hukuncin daurin rai da rai, ga rashin lafiya, da kuma bakin talauci da sauran wasu abubuwa da suke fuskanta da ba za a iya kwatantawa ba.
Kamar dai hakan ma bai isa ba, sama da yaran Nijeriya miliyan 24 ne ke gudanar da aikatau (ayyukan karfi da suka sha karfinsu) a shekarar 2022, inda miliyan 14.3 ke gudanar da ayyuka masu hadari, a cewar hukumar kididdiga ta kasa.
Yawancin wadannan yara masu kananan shekaru suna aiki a wuraren ma’adinai masu hadari da masana’antu, ana amfani da su a matsayin tushen arha saboda kudi kalilan ake biyansu, ba kamar manya ba, inda hakan yake hana su samun ilimi, nishadi da walwala da sauran muhimman abubuwan da za su sanya su a cikin farin ciki da ke tattare da yarintarsu.
Wadannan ba kididdiga ba ne kawai ko shata lambobi, manuniya ce ga matsalolin da suka yi wa yara katutu wanda matukar ba a yi wa guru hanci ba, akwai matsala da kuma cikas ga makomar Nijeriya a matsayinta na kasa.
Yayin da miliyoyin mutanen kasar nan ke fuskantar tauye hakkinsu na samun rayuwa mai inganci, rashin makaranta, auren dole, da ayyuka masu hadari, ta yaya kasar za ta iya samar da ‘yan kasa masu ilimi, masu karfin gwiwa da ake bukata don bunkasa tattalin arziki, mulkin dimokaradiyya da ci gaban zamantakewa?
Al’ummar da ta kasa zuba hannun jari a cikin matasanta, tabbas tana asarar dimbin damarta ta habaka jarin Dan‘adam.
Yayin da aka samu ci gaba mai kyau – kamar samun jihohi 34 daga cikin 36 na Nijeriya da suka amince da dokar kare hakkin yara don yaki da cin zarafinsu – amma kuma babu wani katabus wajen aiwatar da dokar domin kare yaran daga fitinar da ke bazaranar tagayyara rayuwarsu.
A bayyane yake, a ra’ayinmu, ana bukatar kwararan matakai da kuma sadaukarwa daga mahukuntan kasa wajen ba da fifiko ga ‘yancin yara, tsaro da walwala.
Dole ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da tsaro a cibiyoyin ilimi ta yadda za su zamo yankuna masu aminci, da kara yawan jami’an tsaro da kuma bin diddigin jami’an da ba su tabuka wani abin a zo a gani a kan kula da makarantu.
A yi kokarin hadin gwiwa tare da mara bayan kasafin kudi mai ma’ana domin habaka kai yara makarantu, kawar da aikatau na yara, kawo karshen aurar da yara, da kuma magance tushen matsalolin al’umma da tattalin arziki wadanda suke jefa yaran Nijeriya cikin hadari.
Nuna gazawa kawai ba abu ne da ya dace ba – domin idan har wannan al’ummar ba za ta iya kare kyakkyawan fatan da take da shi ba, da kula da makoma da muhimman hakkoin ‘ya’yanta a yau ba, to za ta illata kanta a gobe, ta kuma kara fadawa cikin talauci da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka nan ya zama wajibi ‘Yan Nijeriya su sanya ido sosai kan kalubalen da ke fuskantar yara da matasan kasar nan.
Ta hanyar kare ‘ya’yanta a yau, Nijeriya za ta kare dimokuradiyyar da ta zaba a matsayin turbar ci gaba da kuma damar da za ta samu na ci gaba a Afirka da duniya. Amma ba da fifikon da ya dace ga gina rayuwar yara shi ne babban sinadarin cimma wannan nasara.