A lokacin da Shugaba kasa, Bola Tinubu ya dare kan karagar mulkin Nijeriya, ‘yan Nijeriya da dama suka fara fatan ganin wahalhalun da suke ciki za su kau, musamman ganin cewa a wancan lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta gaza yin abubuwan da suka kamata.
Zaton da ‘yan Nijeriya suka yi wa Tinubu ba ya rasa nasaba da kokarinsa a lokacin da ya yi gwamnan Jihar Legas, kenan zai yi wahala ya gudanar da mulkinsa kamar na Buhari.
- Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Dawo Da Tsohon Taken Nijeriya
- Ranar Yara Ta Duniya: Inganta Rayuwar Yaran Nijeriya Shi Ne Abu Mafi Girma – Tinubu
Sai dai akasarin tsare-tsare da Tinubu ya zo da su sun kara sanya ‘yan Nijeriya cikin wahalhalu fiye da ba, inda har mutane masu rufin asiri wanda a baya suke dan lallaba rayuwarsu, wannan gwamnati ta tagayyara su sakamakon tsare-tsarenta.
Idan aka duba matakinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayun 2023, kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe, duk da yake dukkanin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun PDP da LP sun yi alkawarin janye tallafin mai idan sun sami nasara.
Tinubu ya ayyana janye tallafin mai kwata-kwata a jawabin amsar mulki da ya yi, inda ya nuna cewa za a yi amfani da kudaden da ake bayar da tallafin ne wajen zuba jari a bangaren gine-gine da ilimi da kula da lafiya da samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.
Tun da aka janye tallafin mai fetur, farashin kayayyaki suka fara hauhawa ba kaukautawa, a cewar Tinubu da bai cire tallafin mai ba da yanzu kasar ta talauce.
A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya suke fama da raunin janye tallafin mai, sai kuma gwamnatin Tinubu ta kawo wani tsari a kan darajar naira ko da yake wannan ma yana cikin alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe.
Gwamnati ta bayar da tallafi a matsayin rage radadin halin da mutane suke ciki, wanda za a iya cewa tallafin bai kai inda ya kamata ba, sannan gwamnati ta bayar da umurni a fitar da hatsi da rumbunanta a rarraba wa talakawa, amma mutane da dama ba su sami wannan tallafin ba, ko da yake wasu sun bayar da tabbacin cewa babu komai a wadannan rumbunan da gwamnati ta bayar da umurnin a bude a raba wa al’umma.
A bangaren gwamnati kuwa, kullum tana bai wa ‘yan Nijeriya uzurin cewa tana daukan wadannan matakai ne don inganta tattalin arzikin Nijeriya, kuma a cewarta nan ba da jimawa ‘yan Nijeriya za su dara.