LBisa kididdigar da shafin yanar gizo mai bayani kan hare-haren bindiga na Amurka da aka san shi da suna Gun Violence Archive ya samar, an ce, yawan harbe-harben bindiga da suka auku a shekarar 2023 ya kai a kalla 654, inda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin dubu 43, wato kwatankwacin mutuwar mutane 117 a kowace rana. Duk da haka, sakamakon yadda jam’iyyun siyasa na kasar suke maida kudade da moriyarsu ta fannin siyasa a gaban komai, sun yi kunnen uwar shegu kan abubuwan da ke faruwa ga jama’ar kasar, inda suka gaza kai wa ga cimma matsaya daya kan kayyade yawan bindigar da ‘yan kasar ke mallaka, lamarin da har ya sa al’ummar kasar suke yin hasarar rayukansu. A hakika, hakkin dan Adam na al’ummar kasar ba shi da muhimmanci ga ‘yan siyasar Amurka, kuma hakkin Bil Adam da suke yin shelar karewa dabara ce kawai ta samun kuri’u wajen zabe, balle ma hakkin Bil Adam na al’ummomin sauran kasashe. (Mai zane da rubutu: MINA)