• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NEMA Ta Raba Kayan Tallafi Ga ‘Yan Hijira 24,000 A Katsina

by Yusuf Shuaibu
3 years ago
NEMA

Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta raba kayan tallafin ga ‘yan gudun hijira 24,000 da barnar ‘yan bindiga ta shafa a Kananan Hukumomin Jibiya da Mani da ke Jihar Katsina.

Kayan tallafin da hukumar ta raba sun hada da abinci, buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 10 guda 13,000, da katan na tumatir 120, da katan na sinadarin dandanon girki 120, da jarkunan man girki mai cin lita 20 guda 120 da kuma buhunan gishiri mai nauyin kilogiram 20 guda 120.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Zartar Da Dokar Hana Acaba

Da yake jawabi a yayin rabon kayan, Darakta Janar na NEMA Mustapha Habib Ahmed wanda Babban Jami’in Bayar da Tallafi da Tsugunarwa na Hukumar a Shiyyar Arewa Maso Yamma da ke Kaduna, Kasimu Muhammad Jere ya wakilta, ya yi bayanin cewa tallafin wani bangare ne na taimakon da NEMA ke bayarwa a madadin Gwamnatin Tarayya domin rage wa mutanen da suka rasa matsugunansu radadin da suke ji.

A jawabinsa a madadin Gwamnatin Jihar Katsina, Babban Daraktan Hukumar Bayar da Tallafin Gaggawa ta Jihar (SEMA), wanda wani Darakta a hukumar, Yunusa Mahuta ya wakilta, ya yaba wa NEMA bisa karamcin da ta yi, tare da isar da godiyar gwamnatin jihar.

Da yake mayar da jawabi a madadin ‘yan gudun hijira a Karamar Hukumar Mani, dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Wakilai ta Kasa, Alhaji Aminu Ashiru Mani ya yi godiya ta musamman ga NEMA bisa bayar da tallafin.

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

Har ila yau, shi ma wani shugaban al’umma da ya yi magana a madadin ‘yan gudun hijira na Karamar Hukumar Jibiya, Alhaji Kabiru Mashe, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa yadda ta dube su da idon rahama ta hannun NEMA.

Tallafin kayan dai an raba wa ‘yan gudun hijira da ke garuruwan Shimdida, Garin Mai Wuya, Tsambe, Garin Zango da Kwari da ke Kananan Hukumomin Jibiya da Mani a Jihar Katsina.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!
Rahotonni

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato
Labarai

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki
Labarai

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
Next Post
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Aike Da Tsohon Akanta-Janar Gidan Yari

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Aike Da Tsohon Akanta-Janar Gidan Yari

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.