Fadar shugaban ƙasa ta nuna rashin amincewa da buƙatar ƙungiyar ƙwadago na neman ƙarin mafi ƙarancin albashi na ₦494,000, inda ta yi gargaɗin cewa hakan zai durƙusar da tattalin arzikin Najeriya.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ne ya bayyana irin illar da hakan zai iya haifarwa yayin wata hira a gidan Talabijin na TVC, yana mai jaddada cewa irin wannan ƙarawar zai tilastawa kananan ‘yan kasuwa da dama rufe, wanda hakan zai kara ta’azzara rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arziki.
- Ma’aikatan Shari’a Sun Janye Yajin Aiki A Osun
- ‘Yan Sanda Sun Kashe Dan Bindiga 1 Da Dakile Wani Hari Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Ngelale ya ƙara da cewa shirin ƙarin albashin da ake shirin yi wanda ya ninka kusan sau 20 a matsayin mafi ƙarancin albashi a halin yanzu, zai ɗora wa ƙananan ƴan kasuwa wani nauyi da ba zai ɗore ba, wanda hakan zai haifar da rufewar kamfanoni da kuma asarar ayyukan yi.
Ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar sakamakon ƙin amincewar da kuɗin da gwamnatin tarayya ta ce zata biya na mafi ƙaranci ₦60,000.