Ministan Yada Labarai da Al’adu na Kasa, Lai Mohammed, ya ce babu wata matsalar rashin tsaro ga kasuwanci a Nijeriya, duk da kamfe din da ‘yan adawar siyasa ke yi wa kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne a wani bikin baje kolin masu saka hannun jari mai taken “Africa Walk”, wanda kungiyar UNICORN ta shirya a harabarta da ke Legas a ranar Juma’a.
- Kotu Ta Dage Shari’ar Wanda Ake Zargi Da Auran Jikarsa A Zamfara
- Dokar Da Ta Tanaji Damar Samar Da Rukunin Ababen Hada Na’urorin Laturoni Ta Amurka Za Ta Haifarwa Kasar Da Cikas
Masu kashewa kasar kasuwa kuma na nan na yada labaran karya da ‘yan kasuwar ke yadawa cewa Nijeriya na cikin yaki ko kuma a na tauye hakkin yin addinai.
Mohammed, ya ce gwamnatin Buhari ta hau mulki ne a 2015 da alkawarin gyara tattalin arziki, yaki da rashin tsaro da kuma dakile cin hanci da rashawa kuma gwamnatin ta taka rawar gani a kan alkawura ukun nan.
“An zabe mu ne a kan ginshikan tattalin arziki guda uku, tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa.
“A cikin wadannan wurare uku, ina tabbatar da cewa duk mun cika alkawarinmu, duk da dimbin kalubalen da ake fuskanta,” in ji shi.
Yayin da yake magana kan tsaro, ministan ya ce Boko Haram da ke rike da yankuna masu yawa a yankin Arewa maso Gabas kafin zuwan wannan gwamnati ta fara tasamma zama tarihi sosai kuma an kawar da shugabancin ISWAP.
Ya ce ‘yan tada kayar baya dubu 51 ne suka mika wuya a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar kadai, yayin da a yanzu gwamnati ta maida hankali wajen gyarawa da sake gina al’ummomin da ‘yan ta’addan suka daidaita.
Sai dai wadannan kalamai na ministan ba sh kwantawa wasu a rai ba, inda wasu ke ganin gara gwamnatocin baya da suke shude a kan ta Buhari.