Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar Nijeriya kai tsaye a ranar Laraba 12 ga watan Yuni, 2024, da karfe 7 na safe domin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Lallai A Kamo Makasan Dutsinma da Kankara A Katsina
- Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade
Don haka ne ake ƙarfafar gidajen talabijin, rediyo, da sauran hanyoyin sadarwa na zamani da su haɗa kai don yaɗa jawabin wanda hukumar gidan Talabijin ta ƙasa (NTA) da hukumar gidan Rediyon Tarayya (FRCN) zasu watsa.