Jam’iyyar PDP ta zargi jam’iyyar APC da janyo wa ‘yan Nijeriya wahala, inda ta yi iƙirarin cewa jam’iyyar APC ta gurgunta tsarin Dimokaraɗiyyar da MKO Abiola ya yi yaƙi don kafuwarta. A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar, jam’iyyar PDP ta buƙaci ƴan Nijeriya da su yi zanga-zangar nuna adawa da tsarin Dimokuraɗiyyar jam’iyyar APC a yayin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta bana.
Jam’iyyar PDP ta caccaki jam’iyyar APC da tauye kundin tsarin mulki, da magudin zabe, da danne ‘yan adawa, da kuma raunana cibiyoyin dimokuradiyya.
- Sarkin Kano Na 15 Ya Umarci Hakiman Da Ke Goyon Bayansa Su Halarci Hawan Sallah
- Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025
Ta yi Allah-wadai da ƙaddamar da katafaren gida na Naira biliyan ₦21b ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, adaidai lokacin da ake fama da durƙushewar ababen more rayuwa a ƙasar da kuma yawan rashin aikin yi.
Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi tunani a kan halin da al’ummar ƙasar ke ciki, wanda ke nuna rashin jin daɗin jama’a kan yunwa da tsadar rayuwa, da kuma gyara manufofin da ke cutar da ‘yan kasa.
Sanarwar ta jaddada cewa ya kamata dimokuradiyya ta ba da fifikon ra’ayin jama’a, bin doka da oda, da kuma jin dadin ƴan ƙasa, inda ta zargi APC da yin watsi da waɗannan ka’idoji.