Ƴan fashin daji sun tursasa wa al’umman Bassa, wani kauye da ke da dimbin manoma a Jihar Neja yin kaura daga gidajensu, biyo bayan mummunar harin ta’addanci da suka kai musu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 20.
Sanatan da ke wakilar mazabar Neja ta gabas, Sani Musa, shi ne ya sanar da mummunar labarin yayin da ke magana kan kisan matasa da al’umma 20 a kauyen Bassa da ke karamar hukumar Shiroro.
- Sarkakkiyar Zargin Da Gwamnatin Abba Ke Wa Ganduje
- Kaso 96.4% Na Sana’o’in Kasuwanci Na Sin Mallakin Sassa Masu Zaman Kan Su Ne
Sanatan ya ce maharan sun kashe matasa 10 da wasu mazauna 10 bisa zargin cewa sun ki amincewa su shiga cikin kungiyar ‘yan bindigan.
“Mako uku kawai da suka wuce, kungiyar ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Ku-chi, inda suka kashe jami’an tsaro bakwai tare da yin gaba da mutane kusan 150.
“Har zuwa yanzu kauyen Kuchi ta kasance babu kowa. Wannan sabbin hare-haren na zuwa ne a lokacin da mutane suke kokarin komawa gona domin noma, kuma noman nan shi ne kawai sana’ar da suka dogara da shi,” ya shaida.
Rahotonni sun yi nuni da cewa harin baya-bayan nan da ‘yan fashin daji suka kaddamar a ranar Alhamis a kauyen Bassa da ke Jihar Neja ya janyo rasa mutane 20, lamarin da ya kara tayar wa jama’a hankali.
Su dai ‘yan bindigan sun nemi matasa goma da su shiga cikin kungiyarsu, yayin da suka yi turjiyar cewa ba za su zama ‘yan ta’adda ba, hakan ya sanya suka tsaresu da bude ma wasu mutane 10 wuta, inda suka kashe matasan da sauran mutum 10.
Idan za a tuna dai, ita dai wannan kungiyar ‘yan fashin dajin ta kai hari kauyen Al-lawa, inda ta kashe mutane 9 bayan da suka sha karfin sojojin da suke aiki a yankin.
Duk ƙoƙarin ji daga bakin kakakin ‘yansandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun ya ci tu-ra har zuwa kammala wannan rahoton.