Hadisin da muka kawo a makon da ya gabata da ya yi bayani a kan Hajjin Annabi (SAW), yana kunshe da darussa masu yawan gaske.
Wasu malamai sun bayyana cewa Hadisin yana dauke da karatuttuka da fa’idoji masu yawa a kan Hajji.
Malam Alkadiy Iyad ya ce malamai sun yi magana a kan hukunce-hukuncen fikihun da ke cikin Hadisin har sun rubuta littafai a kai. Hatta Abubakar bin Munzir ya yi babban juzu’i da ya fitar da hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda dari da hamsin a cikin Hadisin. Kuma ya kara da cewa da za a kara kula tare da zurfafa bincike a ciki, za a kara fitar da wasu hukunce-hukuncen.
- Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
- Hajjin Bana: Muna Alfahari Da Goyon Bayan Gwamnan Kaduna– Abubakar Yusuf
Malamai sun ce akwai shiryarwa a cikin Hadisin cewa, yin wanka yayin haramar Hajji yana daga cikin sunna. Hatta ga matan da ba su da tsarki, masu jinin haila ko na haihuwa sunna ne su yi wannan wankan. Za a yi abubuwa na Hajji tare da su, sai dai ba za su shiga Masallaci ba, ba za su yi Dawafi ba. Amma za su je Arfa, su yi kwanan Muzdalifa, da Jifa.
Haka nan, Hadisin ya nunar da cewa yin kunzugu (nafkin) ga mai haila ko jinin biki sunna ne. Sannan za a yi harama da Hajji ne bayan an yi Sallar Farilla ko Nafila (ma’ana bayan mutum ya yi wankan harama ya sanya tufafi na harama, sai ya yi sallah idan lokacin farilla ne ko nafila sannan ya yi niyyar Hajjin). Kuma namiji zai daga murya yayin niyyar (ya yi a bayyane, ba tare da ya boye ba kuma bai cika wa mutune kunne ba).
Bayan haka, Hadisin ya nuna cewa ana so a tsayu a kan Talbiyyar da Manzon Allah (SAW) ya koyar: Labbaikal lahumma labbai…, amma Malamai sun ce idan mutum ya kara a kai ma babu laifi saboda Sayyidina Umar (RA) ya kara da: “Labbaika zanna ama’i wal-fadli alhasani, Labbaika marhuuban minka wa marguuban ilaika.”
Hadisin ya kuma koyar da cewa an so ga Alhaji idan zai fara Dawafi ya fara da sumbantar Hajarul As’wad. Sannan zai yi kewaye uku na farkon Dawafinsa da sassarfa (ba gudu ba kuma ba tafiya ba, tsaka-tsaki). Sauran kewaye hudun kuma zai yi da tafiya.
Wani abu da Hadisin bai kawo ba a nan (amma kuma akwai shi a shari’a) shi ne, idan namiji zai fara Dawafi ya shigo da mayafinsa ta karkashin hammatarsa ta dama, ya zama damtsensa yana waje, sai ya yafo shi ta kafadarsa ta hagu. Ma’ana damtsensa na dama yana waje, na hagu tare da hannunsa kuma suna cikin mayafin.
Bayan kammala Dawafi, sai mutum ya yi Sallar Nafila raka’a biyu a bayan Makamu Ibrahim (a yanzu an lullube wurin da Kwalbar Zinare), raka’a ta farko a karanta Fatiha da Kulya (Suratul Kafiruun), raka’a ta biyu Fatiha da Kulhuwallahu (Suratul Ikhlas).
Har ila yau, Hadisin ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunna ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu.
Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi. Mutum zai hau kan Safa har sai ya ga dutsen, da yake sun rufe shi da gilashi sai a matsa kusa da shi. Idan ya yiwu sai a kalli Ka’aba a ambaci Allah, sannan a yi addu’a. Za a maimaita haka sau uku.
Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka lahu sadaka wa’adahu wa nasara abdahu wa hadamal ahzhaba wahdahu”. Idan mutum bai iya ba, ya yi ta fadin La’ilaha’illallah. Sai ya yi addu’a.
Daga nan ya gangaro zuwa Marwa, a kan hanyarsa zai ga wani wuri da aka sanya koriyar fitila (tsakiyar Safa da Marwa), ana so ya yi sassarfa a wurin. Zai rika yin sassarfar a duk lokacin da ya zo wurin har ya kammala Sa’ayi, ba kamar sassarfar Dawafi da ake yi a kewaye uku ba kawai. Idan mutum ya hau Marwa, a can ma zai yi Zikiri ya yi addu’a.
Hadisin ya nuna cewa idan mutum ya kare Sa’ayi a kan Marwa, to ya kammala Umurarsa sai kawai ya yi aski amma ga mai Tamattu’i.
Bayan ya koma gida zai cigaba da harkokinsa na halas ciki har da kwanciya da iyali wadda aka haramta masa lokacin da ya yi harama har sai zuwa ranar Tarwiyya da za a yi niyyar Hajji.
Wani darasin Hadisin kuma shi ne, duk wanda ya warware haraminsa bayan ya kammala Umura, zai sake yin niyyar Hajji tare da fita zuwa garin Mina. Haka nan shi ma wanda bai warware ba (mai Hajjin Kirani) zai fita zuwa Mina. Sannan yana daga sunna mutum ya yi sallolin farilla guda biyar a can Mina (Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i da Subahi). Kuma mutum zai kwana a Mina (daren ranar Arfa).
Haka nan sunna ce mutum kar ya fita zuwa Arfa har sai rana ta fito, kuma kar ya shiga Arfa sai bayan rana ta yi zawali (lokacin Azahar). Idan mutum yana da kokari, bayan an shiga Arfa sai ya tafi can Masallacin Namira ya saurari huduba; a yi Sallolin Azahar da La’asar da shi lokaci daya. Bayan kammala sallolin sai ya dawo Arfa (hukumomin can sun sanya alamomin da ke nuna kan iyakokin Arfa).
Yana daga sunna Liman ya yi huduba kafin gabatar da sallolin nan (Azahar da La’asar). Wannan ita ce huduba ta biyu, ta farkon ita ce wacce Annabi (SAW) ya yi a rana ta bakwai ga Zhul-Hijja. Akwai kuma huduba ta uku da Liman yake yi ranar Sallah, sai kuma ta hudu a ranar tafiya ta farko (kwana biyu bayan sallah).
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa bayan mutum ya dawo daga sallolin, zai dawo cikin Arfa ya tsaya a kan abin hawansa (idan yana da hali), don haka Annabi (SAW) ya yi. Idan bai samu ba, sai ya zauna ya cigaba da yin Zikiri da addu’o’i har rana ta fadi. Idan mutum ya samu hali ya je wurin da Annabi (SAW) ya tsaya, idan bai samu shi kenan, ko ina (inda aka shata) Arfa ne. Ana so a fuskanci Alkibla yayin tsayuwar ana addu’a. Babu laifi a je a ci abinci ko a dan yawata saboda gajiya duk dai a cikin kewayen Arfar.
Annabi (SAW) ya ce fiyayyen abin da ake karantawa ranar Arfa shi ne: “La’ila’ha’illallahu wahdahu lashariyka lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumiytu wa hul hayyu layamuutu biyadihil khair wa huwa ala kulli shai’in kadiyr”, guda 100.
Bayan an taso daga Arfa sai a nufi Muzdalifa cikin natsuwa ban da gaggawa. Annabi (SAW) ya rika jan akalar abar hawansa har kanta yana taba sirdi domin tafiya a hankali zuwa Muzdalifa. Hadisin ya kuma nuna mutum ya rika horon mutane da natsuwa a yayin komawa Muzdalifa. Da farko shi ya tabbatar da ya natsu, kana sai ya hori wasu da yin hakan.
Idan mutum ya isa Muzdalifa sai ya sauka a nan ya yi Sallolin Magriba da Isha’i a hade (Magriba cikakkiya, Isha’i kasru) ba kuma tare da yin nafila ba. Ana so da an kammala a samu wuri a huta kawai, kamar yadda aka ga Manzon Allah (SAW) ya yi.
Kwanan Muzdalifa na daga cikin sunna, amma an yi sauki ga marasa lafiya ko tsofaffi tukuf-tukuf ko mata masu kiba sosai da ake ji musu tausayin ba za su iya shiga jama’a ba masu yawa, duk sai su yi gaba don su yi Jifa da wuri kana su tafi Makka. Amma matukar mutum lafiyarsa kalau; kar ya yi gaggawa, ya tsaya ya kwana a nan Muzdalifa.
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa sunna ce bayan mutum ya kwana a Muzdalifa bayan ya yi Sallar Asuba sai ya kama hanyar Minna zuwa Masallacin Mash’aril Haram ya dan jira zuwa wayewar gari sannan ya nufi wurin Jifa.
Idan mutum ya zo wurin da ake kira Badanil Muhassar sai ya dan yi sauri don a wannan wurin ne Allah ya halakar da Aburahata sa’ilin da ya zo zai rushe Ka’aba. Amma idan mutum bai san wurin ba shi kenan, dama shi wurin Jifa ya nufa.
A wannan ranar, Jifa daya za a yi na Jamratul Akaba da tsakuwa bakwai (wannan Hadisin ya nuna girman tsakuwar kamar na wake ko gyada wadda ko an samu wani ba za a ji ma sa ciwo ba). Duk lokacin da mutum ya daga hannu zai yi Jifar ya ce Allahu Akbar har ya kammala guda bakwan.
Yana daga falalar Jifar shaidan, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Jifa bai ji (a ransa) cewa an yafe masa zunubansa ba, to a sannan ne ma ya yi laifi.”
Daga nan idan mutum yana Hajjin Kirani ko Tamattu’i ne sai ya nufi wurin da zai yanka dabbarsa, idan ya gama ya yi aski sai ya nufi Makka don yin Dawaful Ifada.
Da zarar ya kammala Dawafin, to komai da aka haramta masa lokacin da ya yi harama ya halasta. Amma idan bai yi wannan Dawafin ba, an halasta ma sa sauran abubuwan da aka haramta wa mai Hajji, sai dai ban da kwanciya da iyali.
Bayan nan sai ya dawo Mina ya yi kwana biyu ko kwana uku. A yayin zaman na Mina kullum mutum zai yi Jifa uku. Daga nan Aikin Hajji ya kare, sai mutum ya je Makka ya yi Dawafin bankwana.
A takaice, wadannan su ne kadan daga cikin darussan Hadisin da Annabi (SAW) ya sanar da cewa duniya ta zo ta ga yadda zai yi Aikin Hajji a shekarar da ya fara yi (SAW).