A yammacin ranar Litinin ne jimami ya ɓarke a unguwar Rimin Kebe da ke ƙaramar hukumar Ungogo a Kano, yayin da aka tsinci gawar wata mata da ba a san ko wacece ba a rataye a gidan Malam Abdullahi Isah, wanda aka fi sani da Malam Auduwa a lokacin ake tsaka da bukukuwan Sallah.
Rahotanni sun bayyana cewa matar ta ziyarci Malam Auduwa ne domin neman taimakon, inda ta bata ruwan addu’o’i, kwatsam bayan wani lokaci sai ta sake dawowa, daga nan sai aka same ta a rataye a banɗakinsa da wata igiya mai kauri a saman rufin ɗakin jikinta ya yi kaca-kaca.
- Gwamnatin Kano Ta Bude Makarantun Da Ganduje Ya Rufe
- Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yin Katsa-landan A Harkokin Kano
Ɗan uwan Malam Auduwa, Rabi’u Isah, ya yi ikirarin cewa matar ba ta taba haduwa da dan uwansa ba, kuma wani mutum ne ya tsinci gawar a lokacin da yake bandaki.
Wani makwabci mai suna Jibril Isah Zango ya tabbatar da cewa Malam Auduwa da dalibansa sun tafi domin sanar da ‘yan sanda.
Matar ta iso tare da ‘ya’yanta guda biyu, inda ta umarce su da su tafi su dawo daga baya, inda ta rataye kanta.
Malam Ilyasu Adamu, Hakimin gundumar Rimin Kebe Gabas ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da aka samu labarin kashe kai a yankin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa har yanzu ba a sanar da ƴan sandan ba amma ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike.