Kungiyar Kaduna Citizens Watch for Good Governance (KCWGG), ta gudanar da zanga-zanga tare da bukatar gwamnatin Kaduna, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai a gaban kuliya bisa zargin karkatar da naira biliyan 423.Â
Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamna Uba Sani da ya sa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta yi bincike kan zargin almundahanar kudi a gwamnatin El-Rufai.
- Rikicin Ƴan daba Yayi Sanadin mutuwar mutum 1, Da Raunata 2 A Kano
- ASUU Ta Bada Wa’adin Mako 3 Ga Gwamnatin Tarayya, Ta Yi Barazanar Shiga Sabon Yajin aiki
Kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gano wasu makudan kudade da suka bace daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Gwamnatin jihar mai ci ta koka kan cewar tana amfani da sama da kashi 70% na abin da jihar ke samu wajen biyan bashin da ta gada daga gwamnatin El-Rufai.
Shugaban KCWGG, Victor Duniya, ya bayyana cewar akwai kudaden da aka karkatar Naira biliyan 10.5 wanda aka ware wa makiyaya da kuma kashe sama da Naira biliyan 11 kan tsarin sufuri na MRT wanda har yanzu babu komai game da shi.
Ya soki gwamnatin El-Rufai da kara yawan talauci a tsakanin al’ummar jihar.
Masu zanga-zangar sun yaba wa Gwamna Sani bisa yadda yake tafiyar sa gwamnatinsa a bude ga kowa don sanin halin da ake ciki.
Sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar an gurfanar da El-Rufai a gaban kuliya, da kuma kwato dukiyar jihar da suke zargin ya yi sama da fadi sa ita.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Balarabe da sauran jami’an gwamnatin jihar sun tabbatar wa masu zanga-zangar cewa sakon nasu zai isa ga gwamnan jihar don daukar mataki.