Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta gargadi Alhazai da su guji debo ruwan Zamzam a matsayin tsaraba a yayin da suke shirye-shiryen dawowa gida Nijeriya.
Daraktan tsare-tsare na hukumar, Prince Anofi Olanrewaju Elegushi ya sanar da haka a yayin da yake ganawa da Alhazan Jihar Ogun a Tantinsu da ke Muna ta Saudiyya, inda ya ce, hukumar Saudiya ta haramta wa Alhazai jigilar Ruwan Zamzam a mastayin tsaraba zuwa gida Nijeriya, “Maimakon haka hukumar Alhazai ta NAHCON ta yi shirin kai wa duk wani Alhajin Nijeriya, ruwan zamzama lita 5 zuwa gida wanda zai karba da zaran ya sauka a filin jirgin sama” , “Dibar ruwan zamzama a cikin kayan Alhazai yana iya barazana ga yanayin tafiyar jirgin sama a sararin samaniya, saboda hada duk wanda aka kama ya debo ruwan zamzam zai fuskanci fushin hukuma, “ in ji shi.
Ya kuma nemi Alhazai su bi dokar kayyade kaya da aka tanada na kilo 8 a jakar hannu da kuma kilo 32 a babbar jaka, “Dauko kayan da suka wuce wadannan ka’ida na iya sa mutum ya yi asarar kayayyakin gaba daya”, a kan haka ya nemi Alhazai su yi hattara wajen sayen kayayyaki domin kada su jibgo kayan da suka wuce kima.
- Wakilin Sin Ya Yi Bayani Kan Matsayin Sin Kan Kare Hakkin Dan Adam
- Kasar Philippines Na Kara Hauka Kan Batun Tekun Kudancin Kasar Sin
Daga nan ya taya Alhazan murnar kammala aikin Hajji cikin nasara, ya ce, “Dole a yaba da halayyar kirki da Alhazan suka nuna a zaman su na Muna, Arafat da Muzdalifah, musamman ganin ba a samu wata hayaniya ko rikici ba a wannan karon kamar yadda yake faruwa a baya”, ya kuma nemi Alhazan su guji abubuwan da za su iya bada musu aikin su, ya kuma nuna muhimmanci dore wa da darussan da aikin Hajji ke koyarwa a cikin harkokin rayuwar su na yau da kullum, ya ce, dole Alhaji ko Hajiya su kare mutuncin wannan matsayin da Allah ya ba su a rayuwa.
A ziyarar, Prince Anofi Olanrewaju Elegushi wanda ya jagoranci wasu manyan ma’aikatan NAHCON da suka hada da Hajiya Zainab Musa da Dakta Tajudeen A. Oladejo da Farfesa Adedimeji M. Adebola da Alidu Shuttu da Babatunde Odunola da kuma Injiniya Goni Sanda Mohammed, sun ziyarci Tantin Alhazan jihohin Legas da Ogun da Ondo da Osun da Oyo da Kwara da kuma Ekiti, a dukkan inda aka ziyarta Alhazai sun yi tambayoyi inda Prince Anofi Olanrewaju Elegushi ya warware musu amsoshin tambayoyin nasu, tambayoyin da aka fi yi a dukkan jihohin da aka ziyarta sun ta’allaka ne ga yadda Alhazai ba su samu cikakken kudin guzuri na Dala 500 ba kamar yadda suka biya tun a gida Nijeriya sun kuma nemi a samar da karin matsugunnai a Muna, Muzdalifah da Arafat.
A martanins,a ya dora laifin rashin samun kudin guzuri bai daya a kan yadda farashin Dala ke tashi da kuma yadda darajar Naira take faduwa a kullum. Ya kuma nemi Alhazan su yi hakuri da yadda lamarin ya kasance.