Hajiya Zainab Sani, Giwa ta zama garkuwan matan Giwa da ke karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
A lokacin da take zantawa da manema labarai a gidanta da ke garin Giwa, Hajiyar Zainab ta nuna jin dadinta da Allah ya sa masarautar Zazzau ta karramata da wannan matsayi na garkuwar matan Giwa.
- ‘Yansanda Sun Cafke Ɗan Banga Kan Zargin Kashe Mutum 2 Kan Rikicin Gona A Adamawa
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Fasahohin Ai Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2024
Hajiya Zainab ta kara da cewa hakan ya kara mata kwarin gwiwar taimaka wa mata kamar yadda ta saba yi a tsawon rayuwanta. A cewarta, taimaka wa mata shi ne burina a rayuwarta.
Haka kuma ta yabo wa Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli bisa gudummawa da yake ba su a kungiyarsu ta matan Musulmi, sannan ta yaba wa hakiminta Uban Doman Zazzau da shugaban karamar hukumar Giwa, Honorabul Abubakar Shehu Kawal Giwa da kungiyoyin da suke bai wa mata tallafi da ‘yan majalasunsu bisa taimako da suke ba mata da marayu da suke karamar hukumar ta Giwa da sauran wurare baki daya.