Majalisar dokokin Jihar Sakkwato, ta gabatar da kudirin gyara dokar masarautar jihar, wadda za ta sahalewa gwamnatin jihar wajen nada sakaruna da hakimai.
Wannan mataki ya tayar da hankulan masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin addini da na siyasa, inda suka yi gargadin cewa hakan na iya ragewa Sarkin Musulmi karfin ikonsa da kuma tasiri a matsayinsa na jagoran addinin Musulman Najeriya.
- Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Shiga Ganawar Sirri Kan Matakin Da FEC Ta Ɗauka
- Bangaren Dawowa Na Kumbo Chang’e-6 Ya Dawo Doron Duniya
Wannan na zuwa ne bayan rikicin masarauta a Jihar Kano, inda gwamnatin jihar ta soke dokar masarautun jihar ta 2019, tare rushe sabbin masarautun jihar hudu da kuma tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan.
Ana zargin gwamnatin jihar ta fara yunkurin tsige Sarkin Musulmi, amma gwamnatin ta yi watsi da wadannan ikirari da zargin.
Duk da tabbacin da Kwamishinan Yada Labarai na jihar ya bayar, na cewa ba a yi wani sauyi a kan dokar nadin sarakunan gargajiya ba, amma lamarin na ci gaba da tada kura.
Babban Daraktan MURIC ya jaddada matsayin Sarkin Musulmi a matsayinsa na shugaban gargajiya da addini, amma wasu jiga-jigai irin su mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da jam’iyyar PDP sun yi gargadi kan yunkurin tsige Sarkin.