‘Yansanda a Jihar Katsina sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara.Â
Kakakin ‘yansandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan a ranar Juma’a cewa, mutane biyu da ake zargi ana musu tambayoyi.
- Wang Yi Ya Yi Jawabi A Liyafar Murnar Cika Shekaru 70 Da Fitar Da Ka’idoji 5 Na Zaman Tare Cikin Lumana
- Zargin Tube Sarkin Musulmi: Kallo Ya Koma Sakkwato
Ya bayyana cewa a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 1:30 na dare, hedikwatar ‘yansanda ta Danja ta samu rahoton masu garkuwa da mutane sun shiga gidan Hauwa’u Adamu mai shekaru 75 a kauyen Kahutu da ke Jihar Katsina, inda suka sace ta.
DPO din ‘yansanda na yankin Danja ya jagoranci wata tawaga zuwa wurin da lamarin ya faru don kama masu garkuwa da mutanen tare da ceto mahaifiyar mawakin.
A yayin binciken, an kama wasu mutane biyu da ake zargi kuma ana yi musu tambayoyi.
Rarara, shi ne shugaban mawakan shugaban kasa a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wakokinsa sun taimaka wajen tara wa shugaba Bola Ahmed Tinubu magoya baya, musamman a tsakanin yankunan Hausawa a Nijeriya.