‘Yan gudun hijira a Karamar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja sun koka kan yadda ‘yan ta’adda suka mayar da yankinsu sansaninsu na dindindin, inda suka shiga suka yayyanka musu kaji gami da daka sakwara da kuma kwashe kayan abincin da suka tanada a cikin shagunansu.
Da yake zantawa da manema labarai a Kuta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Ahmed Almustapha, wani dan gudun hijira daga Rumace-Madalla, ya koka da cewa yayin da suke fama da yunwa a sansaninsu, ‘yan ta’adda sun ci sun cika cikinsu abincin da suka tanada da dabbobinsu.
- Yadda Gidan Buhari Ya Zama Fadar Ziyarar Jiga-jigan ‘Yan Siyasa
- Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)
“Ba mu da jami’an tsaro a cikin al’ummarmu tun bayan janye sojoji daga Allawa. Tun daga wannan lokacin wadannan ‘yan ta’adda sun shafe kwanaki suna kashe mutane fiye da kowane lokaci. ‘Yan fashin sun mayar da yankinmu gidajenssu, su kwana a can suna cin abincin da muka bari a gida. Suna yanka mana kaji su yi miya da su, sannan su cinye mana doya, duk da haka har yanzu ba mai kalubalantar su.
“Tun bayan janyewar wadannan sojoji, mun yi asarar akalla mutu, 50; kuma da yawa an yi garkuwa da su. Makonni uku da suka gabata, an yi garkuwa da mutum 30 a Kauyukan Karaga, Kiriga da Agwaja; kuma har zuwa wannan lokacin, barayin ba su tuntubi kowa ba. Ba mu san inda suke ba ko kuma abin da suke yi da su,” in ji shi.
Rabi’u Iliyasu daga Garin Bassa ya ce duk ‘ya’yansa ba sa zuwa makaranta ne saboda ba shi da wani abin da zai sake daukar nauyin karatunsu.
Ya ce, “Duk ’yan uwana suna tare da ni a sansanin. Wasu daga cikin al’ummarmu suna Erena, yayin da wasu suka gudu zuwa sansanin Gwada. Ina tare da matata a sansanin Kuta. ’Yata tana karatau a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kuta yayin da wasu kuma suna sauran makarantu. Na janye su ne saboda babu abin da zan daukar nauyin karatunsu.
“Ina da ‘ya’ya 17 da ke tsakanin shekaru 7 zuwa 13 da ke karkashin kulawata, ciki har da marayu da aka kashe iyayensu.
“A halin yanzu, ina wasu kananan ayyuka domin tsira da mutuncina. An yanka mahaifin daya daga cikin yaran da suke tare da ni kwanan nan. An yi garkuwa da mahaifiyar daya daga cikinsu shekaru uku da suka gabata bayan kashe mahaifin; kuma har yanzu ba mu ji komai game da ita ba. ‘Yan bindigar sun bukaci Naira miliyan 3 da babur a matsayin kudin fansa, mun biya su har ma da babur amma ba su sake ta ba. Daga baya mun samu labarin an kashe ta ne bayan an kai musu Naira miliyan uku da babur,” in ji shi.