A kwanan nan na karanta wani rahoto mai ban sha’awa da ya yi bayani a kan yadda karancin malaman darussan turanci da lissafi ke kassara samun ilimi mai inganci daga tushe.
Abokin aikina da ya rubuta rahoton, Samuel Abulude ya zakulo matsalolin da suke addabar ilimi da kuma kwazon dalibai a makarantun Firamare da Sakandare a Nijeriya, inda ya dora alhakin lamarin a kan karancin Malaman Turanci da na Lissafi a makarantun fadin tarayyar Nijeriya.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta
- Wani Alhaji Ya Sake Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta A Makkah
Ba abin da za a boye ba ne batun rashin ingancin ilimi a Nijeriya, domin kuwa a shekarun da suka gabata; kasafin kudi na shekara-shekara na gwamnatocin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi, ya yi matukar raguwa, musamman idan aka duba shawarar kason da majalisar dinkin duniya da hukumominta suka ba da shawarar a rika ware wa sashen na ilimi.
Hukumar ilimi, kimiyya da al’adu ta majalisar dinkin duniya (UNESCO), ta ba da shawarar mambobin hukumar su ware kashi shida na kudaden da suka shigo ko kuma kashi 15 zuwa 20 na kasafin kudin shekara, domin tallafa wa ilimi. Sai dai kamar yadda hukumar ta UNESCO ta bayyana, “Yawancin kasashe har zuwa yanzu ba su aiwatar da wannan shawara da aka ba su ba, wadda za ta taimaka wajen bunkasa ilimi”.
Mafi yawancin manyan makarantun Firamare da Sakandare na fama da wadannan matsaloli, yayin da hukumomin da wadanda abin ya shafa suka yi buris da al’amarin, misali kamar hukumomin Jami’o’i na kasa da kuma na ilimin bai-daya.
Har ila yau, hukumar ilimin bai-daya ta shirya taron kara wa juna sani na tsawon kwana biyu, wanda ya hada kwamitin ilimi na majalisar dattawa da jami’an ma’aikatar ilimi ta kasa, a kan wannan karanci na malaman Turanci da Lissafi, wanda kai tsaye ke shafar ingancin ilimi a dukkanin fadin Nijeriya.
A makarantun sakandare, ana ci gaba da fuskantar wannan matsala ta rashin ingancin koyarwa, wanda hakan ke matukar shafar dalibai tare da yi musu tasiri a rayuwarsu.
Babu shakka, wannan matsala ta zama ruwan dare shekara da shekaru, wanda hakan ya kan yi tasiri matuka a kan matasa masu tasowa a halin yanzu. Duk irin abubuwan da suka koya, walau masu kyau ko akasin haka; na iya yin tasiri a rayuwarsu, domin suna kan wata gaba ce ta zama manyan gobe.
A irin wannan yanayin ne, ake koya musu yadda za su rika yin karatu, ya kasance kuma karatun yana shiga kwakwalwarsu da yadda za su ci abinci da kuma yadda za a reni kwazonsu ta hanyar yin la’akari da yadda suke, sannan da kuma yadda za su kyamaci yin ta’ammali da miyagun kwayoyi da dai sauran makamantansu.
Wata mai makaranta mai zaman kanta a Minna, Jihar Neja Olamide Alalade, ta yi magana ne dangane da lamarin inda ta ce, “batun rashin malaman Lissafi da na Turanci a makarantu, na da alaka ne kai tsaye da rashin daukar matakan da suka kamata a dauka. A cewar tata, kamata ya yi mu sake yin tunani kan yadda zamu rika tafiyar da al’amuranmu kamar yadda sauran kasashen waje ke tafiyar da nasu a kan wannan harka ta ilimi”.
Da take yin karin bayani Alalade cewa ta yi, al’umma na yi wa harkar ilimin rikon sakainar kasha, ko kuma sha yanzu magani yanzu, maimaikon daukar matakan da suka dace; wadanda za su taimaka wajen cin moriyar al’amarin kwarai da gaske.
Magana ta gaskiya ita ce, gwamnati da sauran al’umma ya kamata su bada gudunmawar da ta dace, musamman wajen bayar da gudunmayar kudade, domin ilmantar da ‘ya’yansu.Ta ce, “koma me al’umma suka yi; indai bat a da niyyar sa kudade da yawa a wannan bangare na ilimi; a nan gaba, wato shekaru masu zuwa babu wani abin kirki da za a sa ran gani, domin duk wasu abubuwan da aka fara ba za a dauke su da muhimmanci ba, illa ma daga karshe a samu sun lalace’’.
Hadin Sabulu Na Musamman