Asalin rayuwar aure na tsayuwa ne dalilin so da kauna, da tausayi da fahimtar juna, da kyakkyawar mu’amula, da taimakekeniya a tsakani. Kamar yadda Malamai suka yi ba-yani game da wannan batu, Sabani a aure bako ne. Saboda haka kafin a sami sabani wadanne abubuwa ne suke kawo shi a cikin rayuwa ta aure? domin da sanin dalilan samun sabani ko matsaloli ne za a gujewa matsalolin.
Dalilan samun sabani ko matsala a zaman aure:
- Barazanar Da Rashin Katabus Na Kananan Hukumomi Ke Yi Ga Dimokuradiyyar Nijeriya
- Mutane 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Su Da Hannu A Sace Mahaifiyar Rarara
1. Dawwamar mummunan fahimtar juna.
2. Bayyana sirrin dalilin sabanin ga wadanda ba su dace ba.
3. Yawan samun sabani a kan abubuwan rayuwa da katsalandan na dangin mace da abokai da kawaye a cikin sabaninsu.
4. Almubazzaranci da rashin tattalin kayan maigida.
5. Kankamo da rashin wadata iyali daidai gwargwado daga maigida.
6. Mummunar alaka da mu’amula ga surukai da marowaciyar mace, fushi da miji idan ya taimaki ‘yan’uwansa da sauransu.
7. Karkatar mace zuwa ga hidimar yara dungurungum, ta bar kula da hidimar maigida.
8. Mummunar mu’amula da tsananin kishi tsakanin abokan zama (Kishiyoyi).
9. Matsalar mace mara godiya da tsananin gasa da takura maigida a kan abin da ba shi da iko.
10. Matsalar maigida maras godiya da yaba wa kokarin uwargida, da rashin kau da kai da rashin yin uzuri.
11. Bambancin addini ko al’ada ko kabila ko yare tsakanin ma’aurata.
12. Bambancin tattalin arziki, tsakanin ma’aurata.
Wasu daga cikin hanyoyin magance matsalolin aure:
Hanyoyin magance matsalolin aure suna da yawa dan sun bambanta tsakanin al’umma, sai dai a duba wasu daga ciki mahimmai wadanda suka hada da:
1. Neman aure da gudanar da shi a bisa koyarwar Addinin Musulunci. Wato namiji ya nemi irin matar da shari’a ta ce ya nema; haka ita ma mace ta so namijin da shari’a ta ce a so shi.
2. Gudanar da rayuwar aure bisa koyarwar Addinin Musulunci.
3. Boye sirrin juna ga ma’aurata, sai idan ya zama dole a bayyana.
4. Fahimtar juna da kawar da kai da yin uzuri da nusar da wanda ya yi kuskure.
5. Karancin fushi da saurin hucewa.
6. Tattauna matsala idan ta taso, domin fahimtarta don gane inda aka sami sabani tsa-kanin juna.
7. Juriya da dauriya da yin hakuri
8. Mace ta zama mai saukin hali da biyayya.
9. Bai kamata a sami sabami a kan abin da ya zama hakkin juna ba ne, kamar kin ciyar da iyali ga maigida, ko mace ta ki yi wa maigida biyayya.
10. Bai dace ga maigida ya dinga zagi ko munana halittar matarsa ko kuma yin rantsu-war saki ba.
11. Tattaunawa tsaknin ma’aurata don samun fahimtar juna a abubuwa na dabi’ar juna don sanin halin juna.
12. Kada maigida ya kaurace wa matarsa sai a cikin gida.
13. Kada mace ta bar gidan mijinta da sunan yaji saboda sabaninta da maigida, ya dace ta tsaya a kawo karshen abin.
14. Boye wa ‘ya’ya sabanin da ke tsakanin ma’aurata.
15. Gaggauta dinke sabani ko baraka, kada a bari ta dade.
16. Bai halatta a daki mace dukan kawo wuka ba, sai dai a rsaya inda Shari’a ta tsaya.
17. Maigida ya zama mai kyakkyawar nasiha da wasiyya da gaskiya.
18. Ya halatta a shigo da mutum na uku mai amana da boye sirri tsakanin ma’aurata, idan an sami sabani domin ya warware shi. Kuma inda da hali, ya zama makusanci, ko a kirawo wakili daya daga kowane bangare domin su sulhunta su.
19. Neman izinin maigida a abubuwan da Shari’a ta gindaya a nema kafin a aikata su (fita daga gida, azumin nafila idan yana gari, da sauransu).
20. Dangin miji da na mace su yi kyakkyawar mu’amula ga surukansu. Wadanda ba addininsu ko yare ko kabliarsy daya ba, kada a cusgunawa matar ko mijin.
21. Bai dace saboda bambancin tattalin arziki surukai da ‘yan’uwa su dinga tsananta wa maigida ko matar gida ba.