A yau Lahadi ne aka kammala aikin gina tashar adana narkakkiyar iskar gas, irinta mafi girma a duniya, a garin Yancheng na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin.
Wannan tasha kirar kasar Sin, ta kunshi manyan gangunan adana iskar gas guda 10, wadanda za su iya daukar jimillar narkakkiyar iskar gas har cubic mita miliyan 2.5. An ce za a hada sabuwar tashar da yankuna masu samar da iskar gas dake yammaci da arewacin kasar, ta manyan bututun jigilar iskar gas. Kana bayan tashar ta fara gudanar da cikakkun ayyuka, za ta iya sarrafa narkakkiyar iskar gas har ton miliyan 6 duk shekara, kwatankwacin cubic mita biliyan 8.5 na iskar gas.
Ta haka, tashar za ta taka muhimmiyar rawa, a kokarin tabbatar da tsaron makamashi ga manyan biranen dake gabashin kasar ta Sin, da taimaka musu wajen raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. (Bello Wang)