Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta kama hanyar rugujewa sakamakon rashin isassun kuɗaɗen gudanarwa daga gwamnatin jihar.
Shugaban ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen UMYUK Dakta Murtala Abdu Kwara ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsina.
Ya ƙara da cewa maganar da ake yanzu jami’ar na kokowa da matsalar rashin wadatattun kuɗaɗen gudanar da ɓangaren ma’aikata da kuma ɗalibai.
- Mutum 2 Sun Kamu Da Cutar kwalara A Katsina
- Me Ke Shirin Faruwa Tsakanin Sarkin Katsina Da Gwamnan Jihar?
A cewar Dakta Murtala Abdu Kwara gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa na ba wa jami’ar Naira miliyan ₦7m duk wata a matsayin kuɗin gudanarwa a maimakon miliyan 16 da ake bata a gwamantin da ta gabata.
“Wannan jami’a ta fara karatu ne da tsangaya uku ne kacal da kuɗin gudanarwarta miliyan 16, yanzu kuma muna da tsangaya 9 amma kuɗin gudanarwa ba su canza ba, suna nan miliyan 7″ inji shi
Ya ce halin da jami’ar take ciki a halin yanzu ta sa dole aka dakatar da baiwa sassan jami’ar kuɗaɗen gudanarwa.
Haka kuma ya koka kan yadda gwaman Dikko Umar Raɗɗa ya ƙi aiwatar da kaso 25/35 na albashin ma’aikata wanda ya ce wasu jami’o’i tuni sun fara aiwatarwa.
Kazalika Dakta Murtala Abdu Kwara ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina ta sake duba tsarin biyan kuɗaɗen gudanarwa na jami’ar domin ceto ta daga durƙushewa.
Duk wani ƙoƙari domin jin martani daga bakin Kwamishin ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar Katsina Farfesa Abdul Hamid Ahmad ya ci tura kafin kammala haɗa rahoton.