ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Wajen Najeriya: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Samarwa Afirka Damammakin Ci Gaba

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 years ago
Sin

Ministan ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya Yusuf Maitama Tuggar, ya ce karkashin manufofin kasar Sin da suka hada da dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, da shawarar ziri daya da hanya daya, Sin ta samarwa kasashen Afirka ciki har da Najeriya, wasu damammakin samar da ci gaba na musamman.

Tuggar, wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da ‘yan jaridar kafar CMG a kwanan baya, lokacin da yake ziyarar aiki a kasar Sin, ya ce Najeriya na aiki tukuru wajen ingiza hadin gwiwa da Sin a fannoni daban daban, wadanda suka hada da raya layukan dogo, da hanyoyin mota, da bututan iskar gas da lantarki. Ya ce Sin ta zuba jari mai tarin yawa a fannin gina ababen more rayuwa, wanda hakan ya ingiza damar samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan Najeriya, kuma hakan ya yi matukar amfanar kasar.

  • Kasar Sin Ta Amince Da Dokar Ba Da Agajin Gaggawa Da Aka Yi Wa Kwaskwarima
  • Yadda Rangers Ta Lashe Gasar Firimiyar Nijeriya 

Ministan ya kara da cewa, nahiyar Afirka na bukatar karin jari mai tarin yawa, domin bunkasa fitar da hajojin da aka sarrafa a cikin nahiyar, ba wai kawai kayan da ake fitarwa domin a sarrafa a waje ba. Kuma kasar Sin ta tabbatar da kudurin ta na taimakwa wajen warware wadannan matsaloli, ta kuma nuna matukar goyon bayan ta ga Afirka, ta hanyar juba jari mai yawa a nahiyar.

ADVERTISEMENT

Ya ce bisa yadda kamfanonin Sin ke shiga ana damawa da su, sashen sarrafa batiran lithium na Najeriya na kara fadada. Kaza lika hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin sabbin makamashi, zai fadada cin gajiya daga sassan daban daban masu nasaba, ciki har da na kirar ababen hawa masu aiki da lantarki. Kuma baya ga kasuwar cikin gida ta Najeriya, fannin zai kuma samar da hajojin fitarwa zuwa sauran kasashen duniya. Hadin gwiwar sassan biyu zai samar da muhimmin tallafi ga Najeriya a fannin raya masana’antun ta.

Game da batun fasahar kirkirarriyar basira ko AI kuwa, ministan ya ce Najeriya na da matasa masu hazaka, da za su taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da hadin gwiwa da Sin a fannin na AI. Don haka ya yi fatan cewa, kasashen biyu za su fadada hadin gwiwa a fannonin musayar al’adu, da ilimi, da harkokin zamantakewa, da horaswa a fannin samar kwarewa. Mista Tuggar ya kara da cewa, Sin ba ta kallon duniya ta fuskar taswirar yankuna, maimakon haka, tana fatan dunkulewa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda kasashe da yankunan duniya za su kara kusantar juna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • Sulaiman
    Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara
  • Sulaiman
    Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

MASU ALAKA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
Daga Birnin Sin

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
Daga Birnin Sin

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara
Daga Birnin Sin

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Next Post
Jami’ar Yar’adua Da Ke Katsina Ta Kama Hanyar Durƙushewa – ASUU

Jami'ar Yar'adua Da Ke Katsina Ta Kama Hanyar Durƙushewa - ASUU

LABARAI MASU NASABA

Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

July 17, 2026
Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

July 17, 2026
Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

July 17, 2026
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.