Dakarun rundunar hadin gwuiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun kashe ƴan ta’adda sama da 70 tare da lalata wasu bama-bamai da aka haɗa da motoci 8 a wani sumame na baya-bayan nan a yankin tafkin Chadi.
Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar ta MNJTF, Laftanar Kanar Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa, waɗannan hare-haren da aka samu nasara, wani ɓangare ne na Operation Lake Sanity 2, wanda ya haɗa da kai hare-hare ta sama da ƙasa kan sansanonin ƴan ta’adda a faɗin yankunan Kamaru da Najeriya.
- Rundunar Sojojin Kasar Sin Ta Ci Gaba Da Yin Atisayen Soja a Wuraren Dake Kewayen Tsibirin Taiwan
- Rundunar Sojoji Ta Karrama Mace Ta Farko Da Tayi Karatun Zama Soja A UK
A yayin farmakin, dakarun MNJTF tare da goyon bayan rundunar sojojin ƙasar Chadi cikin gaggawa sun tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda guda biyar tare da kashe ƴan ta’adda 70. Sojojin sun kuma lalata wasu manyan makamai guda biyu a arewa maso gabashin Malam Fatori.
Laftanar Kanar Abubakar ya mika godiyarsa ga dukkan Sojojin da suka halarci aikin, waɗanda suka haɗa da na Operation Emergence 4 Kamaru, da Operation Haɗin Kai Nigeria, da Sector 4 Nijar, waɗanda gudunmawarsu ta taka rawa wajen samun nasarar aikin.
Ya kuma jaddada aniyar MNJTF na kawar da ta’addanci da kuma maido da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi, inda ya sha alwashin ci gaba da yin aiki tuƙuru da abokan hulɗa domin cimmawa da kuma ɗorewar wannan muhimmin manufa.