Kudirin da ke neman kirkirar sabowar Jihar Adada a shiyyar kudu maso gabas, a ranar Talatar da ta gabata, ya sallake karatu na farko a zauren majalisar dattawan Nijeriya.
Kudirin wanda aka ambato bisa dogara da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka yi wa garambawul (SB. 482), dan majalisa da ke wakiltar mazabar Inugu ta Arewa, Sanata Okey Ezea ne ya gabatar.
A cewar dan majalisar, kudirin na neman a yi kwaskwarima ga sashi 3(1) da sashi na 1 na kundin tsarin mulkin Nijeriya domin bayar da damar kirkirar wata sabuwar jiha a shiyyar kudu maso gabas.
Wannan yunkurin na da manufar ganin an samu kai jihohin shiyyar zuwa guda shida kamar yadda sauran shiyyoyi suke da shi domin su yi gogayya tare.
Rahotonni sun yi nuni da cewa gwagwarmayar neman kafa sabuwar Jihar Adada dai ya samu asali ne tun daga 1983, a lokacin da Marigayi Sanata Isaiah Ani da ke wakiltar mazabar Nsukka ya gabatar da irin wannan kudirin a gaban majalisar a jamhuriyya ta biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp