Gwamnatin Jihar Kano ta fayyace zare da abawa game da rahoton da ake yadawa a shafukan sada zumunta kan cewar wani jami’in Hisbah a jihar na da alaka da kungiyar ‘yan madigo, inda ta ce ta haramta auren jinsi a jihar.
A wani bidiyo da aka yada ya nuna yadda wani jami’in Hisbah ke bayani game da ‘yancin ‘yan luwadi da ‘yan madigo a jihar.
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- Yawan Motoci A Kasar Sin Ya Kai Miliyan 440
Sai dai Kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi wa ‘yan jarida karin haske a ranar Litinin.
Hisbah ta tabbatar da cewar mutumin da ke bidiyon jami’inta ne, amma ba da yawunta ya halarci taron ba.
Daurawa, ya ce hukumar ta jima tana yaki da maza masu neman junansu, wadanda aka fi sani da ‘yan daudu.
Daurawa ya ce kowa ya san yadda hukumar ke yaki da ‘yan daudu, don ire-iren wadannan kungiyoyi su bar jihar domin ba su da mazauni.
Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya bai wa Hisbah umarnin zakulo ire-iren wadannan kungiyoyi tare da fatattakarsu daga jihar.