Bisa kididdigar da ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karshen watan Yunin shekarar 2024, yawan motoci a kasar Sin ya kai miliyan 440, ciki har da kananan motoci miliyan 345, wadanda suka hada da motocin sabbin makamashi miliyan 24.72, Akwai direbobin ababen hawa miliyan 532 da suka hada da direbobin kananan motoci miliyan 496 a kasar. A farkon rabin shekarar 2024, an samu sabbin motoci miliyan 16.8 da aka yiwa rajista da sabbin direbobi da aka baiwa lasisi miliyan 13.97 a duk fadin kasar. (Mai Fassarawa: Mohammed Baba Yahaya)
Talla